Dandalin fasahar na'ura da kasuwanci online

Dandalin fasahar na'ura da kasuwanci online IB Global Tech is online Technology academy

Amfani da Java (AI) Part 2Fa'idoji da Kalubale na Gina Library (AI)Amma inka dage bazaka sha wahalaba sosaiFa’idoji:Kwar...
20/12/2025

Amfani da Java (AI) Part 2

Fa'idoji da Kalubale na Gina Library (AI)
Amma inka dage bazaka sha wahalaba sosai

Fa’idoji:
Kwarewa da fahimta: Zai taimaka maka sosai wajen fahimtar yadda AI ke aiki a matakin farko.

Cikakakken Iko (Custom): Zaka iya tsara library ɗin daidai da bukatunka.

Ilmantarwa:Wannan zai karfafa fahimtarka game da yadda algorithms k**ar decision trees, neural networks, NLP parsers, da sauransu suke aiki.

❌ Kalubale:

Wahala: Gina library ɗin Deep Learning ko NLP daga tushe yana da matukar wahala kuma yana buƙatar zurfin ilimi.

Lokaci: Yana ɗaukar lokaci sosai idan kai kadai kake yi.

Bug Fixing: Kai zaka lissafa, gwada, da gyara komai da kanka.

🔧 Me Zaka Iya Gina? (Daga Farko)
1. Machine Learning:
Zaka iya gina:

Linear Regression
Decision Trees
KNN (K-Nearest Neighbors)
Naive Bayes
SVM (Support Vector Machine – yana da ɗan wahala)

2. Deep Learning:
Gina neural network daga tushe zai buƙaci:

Matrix operations

Activation functions (ReLU, sigmoid, softmax, da sauransu)

Backpropagation algorithm

Optimizers (gradient descent, da sauransu)

3. NLP (Natural Language Processing):
Tokenization (raba kalmomi)

Part-of-speech tagging

Named Entity Recognition

Syntax tree building

Language model (n-gram, transformers – mai wahala sosai)

4. Robotics/IoT:
Zaka iya amfani da Java don sarrafa hardware ta hanyar Serial Communication da Java Embedded Libraries.

//Misali mai sauki na binary decision tree a Java

class Node {
String question;
Node yes;
Node no;

Node(String question) {
this.question = question;
}

void traverse() {
System.out.println("Q: " + question);

}
}

a darasi na gaba zamuyi bayanin Topic din da kake bukata domin farawa

Amfani da yaren Java a AI Part 1Menene AI (Artificial Intelligence)?AI (Artificial Intelligence), wata fasaha ce da ke b...
20/12/2025

Amfani da yaren Java a AI Part 1

Menene AI (Artificial Intelligence)?
AI (Artificial Intelligence),

wata fasaha ce da ke baiwa kwamfuta ko na’ura damar yin abubuwa k**ar yadda mutum ke yi

Fahimtar harshe (Natural Language Processing)

Koyo daga bayanai (Machine Learning)

Gane fuska ko murya

Yin shawara ko warware matsaloli

SHIN YAYA JAVA YA KE AIKI A HARKAR (AI)

Java ba kawai yare ne na shirye-shirye ba, har ila yau yana da matukar amfani a harkar Artificial Intelligence (AI). Idan ka karanci yaren ka iyasa sosai, za ka iya amfani da shi wajen gina manhajoji masu basirar (intelligent systems).

Java AI – Ta Yaya Java Ke Aiki da (AI)?
Java wani yare ne na shirye-shirye (programming language) da ake amfani da shi wajen gina aikace-aikace. Kodayake yaren Python ne ya fi shahara a AI, Amma Java ya kasance me amfani sosai a bangaren kawai de mutane sunfi mayarda hankaline a shi Python din.

ME YASA JAVA KEDA AMFANI A (AI)

Tsaro (Security): Java yana da kariya sosai daga kuskure.

Yawan Amfani: Yana aiki a kowanne dandali (platform), wato "write once, run anywhere".

Kyakkyawan Salo da Dubara: Yana da tsarin OOP (Object-Oriented Programming) wanda ya dace da ayyukan AI.

Abubuwan da Za a Iya Yi da Java a AI:

Machine Learning (Koyon Na’ura):
Ana amfani da libraries k**ar:

Deeplearning4j – Don Deep Learning

Weka – Don nazarin bayanai (data analysis)

MOA (Massive Online Analysis) – Don Big Data

Natural Language Processing (NLP):

Apache OpenNLP – Don gane yare da sarrafa rubutu

Stanford NLP – Don harshe da tunani

Robotics da Internet of Things (IoT):
Java yana da amfani wajen sarrafa na’urori da robot.

SHIN ZAKA IYA GINA WADANNAN LIBRARIES DA KANKA A JAVA?

Eh, zaka iya gina naka library a Java maimakon amfani da waɗanda aka ambata k**ar Weka, Deeplearning4j, ko Stanford NLP.

Amma yana da muhimmanci ka fahimci:

Fa'idoji da Kalubale na Gina Library da Kanka

A posting na gaba zamuyi bayanin wannan

27/07/2025
B TECHNOLOGY INSTUITEBAYANI AKAN MAKARANTADafarko dai k**ar yadda kuka sani sunann wannan makaranta ( B.T.I ) B TECHNOLO...
29/12/2024

B TECHNOLOGY INSTUITE
BAYANI AKAN MAKARANTA
Dafarko dai k**ar yadda kuka sani sunann wannan makaranta ( B.T.I ) B TECHNOLOGY INSTUITE kuma wannan makaranta ta shirya tsaf domin horar da matasanmu ilimi akan naura,
Karin haske, Kamar yadda wannan duniya ke canjawa kuma zamani ke shudewa, idan munyi laakari da yadda ake ci gaba a duniya, NAURA, INTERNET, sun kawo babban sauyi ga duniya, k**a daga sashen ILIMI, LAFIYA, TSARO, KASUWANCI, HADA HADAR KUDADE, Dama kowanne sashe na rayuwar Alumma. To idan dai hakane yazamai mana dole muyi amfani da duk damar da mukasamu domin ganin munci moriyar wannan babban tagomashi, sannan wannan ilimi ya bunkasa ta yadda matasa suke cin moriyar sa, akwai matasa da yawa da sukeyin kasuwancinsu ko aiki a internet kuma suke samun manyan kudade, kuma halatattu, yan kasuwa da yawa suna kasuwancin su internet kuma suna samun riba mai yawa, !yanzu muna da yan kasuwan da zasu siye kaya a internet batare da suje ko inaba kuma zasu siyar a internet suna gida kuma su sami riba wasu suna tallace-tallace wasu kuma suna kodago, duk daga gida cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, to wannan fagen anyi nisa amma abin takaici mu a arewa haryanzu da sauran kalubale, wannan shine dalilin da yasa zakaga idan kaje bankuna manyan kamfanoni ko kuma wasu hukomomi galibi yan kudu zaka gani, to a arewa muna karancin ilimin, bazan manta da lokacin register national id card ba a wannan lokacin da yawa yan kudune sukayi aikin, shi yasa akaita samun spelling mistake wajan rubuta sunayen mutane,
Duk da dai dayawa matasa suna kokari amma akwai bukatar kara mayar da hankali a fagen dan zuwa gaba komai na iya faruwa,
lokaci yana shudewa nan gaba idan baka da ilimin naura, ba wanda zai daukeke aiki koda kuwa leburanci ne.
Sabida haka yana da kyau lallai muyi kokari muyi amfani da duk damar da muka samu, don ganin mun amfana,

wannan dalilin yasa muka samar da wannan makaranta, domin bayar da irin tamu gudun mawar,

YADDA TSARIN KARATUN YAKE

1. zakayi Registration
2.Dole ka mallaki ID CARD domin dole sai dashi zaka shiga class
3. za'ayi karatu na tsawon wata uku
4. sannan za ayi jarabawa duk wanda yayi nasara za a bashi takardar shaida kammalawa ( CERTIFICATE )
5. Sannan ana karatu da yaren hausa domin asamu saukin fahimta
6. Duka tsarin karatun a ONLINE za'ayishi sannan akwai RUBUTU, DA HOTUNA, VIDEOS, VOICE, HARDA PDF da dai sauran hanyoyin koyarwa na zamani

A YANZU HAKA ANFARA REGISTRATION, KASANCE DAYA DAGA CIKIN DALIBANMU DOMIN CIN MORIYAR WANNAN MAKARANTA,

DOMIN REGISTER KO KARIN BAYANI ZA'A IYA TUNTUBARMU A WANNAN LAMBAR KIRA KO WHATSAPP 0703 368 3932

Makaranta da take koyarwa a yaren hausa
28/12/2024

Makaranta da take koyarwa a yaren hausa

Ilimin Hacking (Kutse) 💻Kamar yadda nake fada maku shima fa hacking ilimi ne wanda sai ka koya zaka iya, bawai cika baki...
13/02/2024

Ilimin Hacking (Kutse) 💻

Kamar yadda nake fada maku shima fa hacking ilimi ne wanda sai ka koya zaka iya, bawai cika baki da hacking din Facebook account din mutane shine hacking ba, wannan kawai dai kana trying amma ba shine ainahin duniyar hacking ba.

Bari kuji; idan kanaso ka zama shahararren hacker to fa sai ka tsunduma wajen karantar bangaren dan'uwa, kuma idan ka koya ka iya to ya zama hanyar da zaka dinga taimakon Addininka, basai na maku dogon bayani ba kungane abinda nake nufi.

Wato kwarewa a hacking yana buqatar ka maida hankali bangaren koyon wadannan abubuwan da zan lissafo guda 10 yanzu in sha Allah.

1. Intermediate Computer Skills; wato yanada kyau ace ka iya kirkirar Word documents ko kuma kana iya surf din web, sannan dole ya kasance kasan yadda zaka dinga amfani da mabanbantan Commands Lines na Windows, ka iya seta network, sannan ka iya Editing din Registry din Computer dinka.

2. Good Networking Skills; wato yawancin hackers sunfi yin ta'adi a Online sunfi yin barna a saman yanar gizo dan haka dole ka koyi ilimin Networking da Terms dinsa k**ar irinsu;

• WEP versus WPS password
• NAT
• MAC Addresses
• Routers
• Ports
• VPN
• IPv6
• DNS
• Subnetting
• DHCP
• Private and public IPs
• Ipv4
• OSI Modelling
• Packets
• TCP/IP

3. Using a Linux operating system; yawancin hackers sunfi amfani da "Linux OS" saboda tana barin programs da tweaks a windows da kuma Mac operating system. Yawancin hacking tools din sunfi aiki acikin wannan operating system din.

4. Virtualization; kafin ka fara qoqarin yin hacking farko kafara sanin menene zakayi kuma ka tabbatar komai kanayin shi akan tsari batareda kuskure ba, kwararren hacker baya barin kuskuren da za'a k**ashi, idan kasamu kwarewa kanaso ka jaraba baiwar naka to karka ce zaka fara da babban aiki, kafara jarabar Hacking dinka ga qaramin abu haka, k**ar "Virtualization Software package" k**ar irinsu; VMWare Workstation. Wajen amfani da Virtual Workstation hakan zai baka damar kayi gwajin fikirarka ta hacking batareda wani hadari ma kuma batareda ka jawo wa computer dinka wata matsalar ba ko lalace wa, sbd idan kana koyo kace zakayi hacking din wani abun bayan baka kware ba to Ido zai raina fata domin kana iya lalata computer dinka.

5. Tcdump or Wireshark; shi dai Tcdump anfi saninsa da Command Line Protocol analyser ko kuma kace Sniffer duk sunansa ne Tool ne na hacking mai dan bala'in sata. Shi kuma Wireshark yawanci mutane sunsan shi shima aikinshi iri daya da Tcdump.

6. Knowledge of security Technologies and concepts; lallai duk hacker yanada buqatar mafi muhimmanci acikin Concept and technologies wanda yake da alaqa da information technology. Saboda haka yanada kyau kasan Wireless Technology And Concepts irinsu; "Secure Sockets Layer" (SSL) Firewalls, Intrusion Detection System (IDS), Public Key Infrastructure (PK) da sauransu.

7. Scripting Skills; kasamu damar iya kirkira da editing din Scripts hakan zai baka damar ka iya kirkirar naka Tool din, ta yadda zaka zama Independent! Kana harkarka ba ruwanka da amfani da tools din wasu, zaka kirkiri kayan aikin da ba kowa yasanta ba kayi amfani da abinka wurin kai hari, to idan kanaso ka kware wajen hakan dole ka maida hankali wajen karantar Scripting language k**ar irinsu; Ruby on rails, ko kuma Python.

8. Database Skills; idan kanason kasan yadda hackers suke kutse su fada cikin rumbun adaba bayanan mutane ko kuma kanaso ka iya hakan to yanada kyau kasan shi yaya ma database din take aiki da sauransu, dan haka yanada kyau ka samu kwarewa a "Database management system" k**ar irinsu; Oracle, ko MySQL.

9. Reverse Engineering; shi wannan zai baka damar ka iya converting piece na malware ko kuma mai k**a da Exploit into more advanced hacking tool.
Daga lokacin da ka fahimci yadda "malware da exploit features suke aiki to tabbas kasamu damar gane yadda ake cikakken hacking din computer.

10. Cryptography; wannan skill din yana baka damar kasan yadda hacker suke samun damar boye kansu idan zasuyi barna ko ta'asa a wani wuri to zaka iya gane yadda suke batar da sawu kaima kuma zaka iya koya, sannan zai baka damar gane mabanbantan weakness algorithm wadanda ake amfani dasu wajen Decrypting Personal information k**ar irinsu; Stored Password.

Allah ya tsare mu da shairinsu 🙏

Kuyi following da like

Yanda ake sauke Gmail daga kan waya (Remove) Idan za a sauke Gmail account daga kan waya ba sign out ake yi ba, ana yin ...
13/02/2024

Yanda ake sauke Gmail daga kan waya (Remove)

Idan za a sauke Gmail account daga kan waya ba sign out ake yi ba, ana yin remove ɗinsa ne, idan akan browser akayi sign in shine ake sign out idan ana son sauke shi. Domin sauke shi daga kan waya ana bin wannan matakan k**ar haka:

- Zaka shiga Settings

- Sai ka nemi inda aka rubuta Accounts sai ka shiga ciki

- Bayan ka shiga zaka ga dukkanin Gmail account da suke kan wannan wayar, sai ka danna wanda kake son saukewa daga kan wayar

- Bayan ka danna zaka ga inda aka rubuta "Remove account" sai ka danna shi, shikenan ka sauke wannan Gmail account ɗin daga kan wayar.

Me tambaya mu had a comment section

YADDA ZAKAYI UNBANNED WHATSAPP DINKA DA AKAYI BANNED NAN TAKE. Idan kabi wannan Step din inshaallah a ƙasa da awa1 zasuy...
23/01/2024

YADDA ZAKAYI UNBANNED WHATSAPP DINKA DA AKAYI BANNED NAN TAKE.

Idan kabi wannan Step din inshaallah a ƙasa da awa1 zasuyi unbanned numbanka.

Da farko dole ka mallaki gmail saboda a cikin gmail zaka tura masu sakon

Zaka Shiga Cikin Email Naka Sai Kayi paste na wannan ko kuma ka rubuta, sai ka shigar da cikon numbanka da akayi banned gaban +234 din nan
👇
Dear Whatsapp Support Team, i am writing to request that my WhatsApp account be unblocked, I recently received a notification that my account has been banned, but I am not aware of any violation of your terms of service. My phone number +234.......

Please review and unbanned my account.

Sai Ka Turawa Wannan Email din.
👇
[email protected]

Shikenan WhatsApp company Zasu turo Maka message bayan mintina zuwa awa1

Suna turo message din kawai Basai Ka karanta Ba
WhatsApp Din Yagyaru.

Wannan da kuke gani ban jima da yi baifi awa1 ba har sunyi unbanned numban.

Allah yasa mu dace🙏

Kuyi follow da like

18/01/2024

MENENE LAMBAR WAYA KUMA YAYANE TAKE AIKI

LAMBAR WAYA ( Phone number )
Idan akace LAMBAR WAYA ana nufin wasu shiryayyun lambobine da ake amfani dasu wajen fahimtar
layin tafi da gidanka, a kuma aiwatar da kiraye-kiraye ko sakon karta kwana,
GINSHIKAN LAMBAR WAYA
1- Country code
2- Network provider code ( mobile network prefix )
3- Area code ( Geographical Codes )
4- Local subscriber number
1. COUNTRY CODE = Wasu killatattun lambobine, da suke zuwa a farkon lambar layi, da suke
wakiltar kasa ko yanki a taswirance
Misali +234 nigeria, +1 united state, +44 united nation etc
Wannan shine misalin Country code
2. AREA CODE = yana nuniga wani killataccen yanki a cikin kasa, area code na temakawa wajen
tasarrufin kira izuwa gurin da yadace
Misali 212 New York 310 Los Angeles
3. NETWORK PROVIDER CODE ( mobile network prefix ) = wadannan kuma wasu lambobine da
suke wakiltar kamfanin layinka misali 0803 NPC ( MTN ) ne
4. Local subscriber number = wasu shiryeyyun lambobine na kai da kai da suke nuni ga mai
mallakar layi a cikin killataccen yanki su local subscriber number suna biyo bayan area code
GA WANI MISALI
Mu dauki wannan lambar 08031234567
Gasu guda goma sha daya
+234 = Country code
803 = Network provider code(MTN)
1 = yana nuni ga region ko area
234567 = Local subscriber number
A Nigeria bamu da area code k**ar sauran wasu kasashe, sai dai lamba guda daya da take bin bayan
network provider code
Ukun farko +234 country code
ukun dake binsu 803 network provider code
saikuma daya dake binsu 1 indicates region ko area
sannan ragowar lambobin guda shida 234567 local subscriber number

Wanne attack ne ka iya
14/01/2024

Wanne attack ne ka iya

Address

Nasarawa Main Market
Nasarawa

Telephone

+2349067511839

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dandalin fasahar na'ura da kasuwanci online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dandalin fasahar na'ura da kasuwanci online:

Share