06/02/2026
SAKON GODIYA TA MUSAMMAN
Kwamitin JIBWIS Social Media na karamar hukumar Dambam na farin cikin mika sakon godiya da jinjina ta musamman ga wata baiwar Allah mai son alheri, wadda ta bai wa kwamitin kyautar sabuwar waya kirar Tecno Spark 40, domin kara karfafa aikin yada karatuka, wa’azozi, da shirye-shiryen ilmantarwa na addini ta kafafen sada zumunta na zamani.
Babu shakka wannan gudummawa ta nuna kishin addini, kaunar al’umma, da kuma fahimtar muhimmancin yada sakon gaskiya a wannan zamani. Irin wannan aiki yana daga cikin sadaqatul jariya wadda ladanta ke ci gaba ko bayan rayuwar mutum.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya saka mata da mafificin alheri, Ya yalwata mata arziki mai albarka, Ya kare ta da iyalanta daga dukkan sharri, Ya kuma sanya wannan kyauta ta zama haske a kabarinta da dalilin samun Aljanna. Ameen.
Haka kuma muna kira ga sauran ‘yan’uwa maza da mata masu hali da su yi koyi da irin wannan abin alheri, domin taimakawa yada ilimin addini da shiryar da al’umma hanya ce ta samun lada mai dorewa a duniya da Lahira.
Allah Ya karɓa, Ya saka da alheri mai yawa. Ameen.
JIBWIS Social Media Dambam
18/Sha'aban/1447
6/2/2026