Aliyu Umar Dandalin labarai

Aliyu Umar Dandalin labarai Please Subscriber my channel mushakata tv https://youtu.be/XWFhJRkfyD0

07/02/2021

Labarai da domin dominsu

LABARINA SEASON 3
07/02/2021

LABARINA SEASON 3

An hana Liverpool shiga Jamus don buga wasan Champions LeagueHukumomi a Jamus sun hana ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpoo...
04/02/2021

An hana Liverpool shiga Jamus don buga wasan Champions League

Hukumomi a Jamus sun hana ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool shiga ƙasar domin buga wasan farko na zagayen 'yan 16 a gasar Champions League da ƙungiyar RB Leipzig saboda cutar korona.

An tsara buga wasan ne ranar 16 ga watan Fabarairu a gidan Leipzig kafin daga baya ma'aikatar cikin gida ta bayar da sanarwar hana tawagar Liverpool shiga ƙasar.

Leipzig ta yi fatan a yi mata alfarma bayan gwamnatin Jamus ta haramta wa 'yan ƙasashen da ke fama da sabon nau'in cutar korona shiga ƙasarta har zuwa 17 ga watan Fabarairu.

Bisa tanadin dokar UEFA, ya rage wa Leipzig ta naemi wani wurin da za a buga wasan, yayin da ake tunanin za a buga shi a birnin Landan.

Wani zaɓin shi ne, ƙungiyoyin za su iya yanke shawarar sauya wurin buga wasan, abin da ke nufin za a iya fara bugawa a Anfield, gidan Liverpool.

Ita ma Manchester City za ta fuskanci Borussia Moenchengladbach a Jamus ranar 24 ga Fabarairu, sai dai ana sa ran za a ɗage haramcin shiga ƙasar kafin loƙacin.

Majalisar Dokokin Amurka ta bukaci Biden ya jinkirta janye sojojin ƙasar daga AfghanistanWani rahoto da ya samu goyon ba...
04/02/2021

Majalisar Dokokin Amurka ta bukaci Biden ya jinkirta janye sojojin ƙasar daga Afghanistan
Wani rahoto da ya samu goyon bayan dukkanin jam'iyyu a Majalisar Dokokin Amurka ya bukaci gwamnatin Biden ta jinkirta shirin janye sojojin Amurka daga Afghanistan.

Jami'an sojin Amurka dubu 25 ne ke shirin ficewa daga kasar nan da watan Mayu, karkashin wata yarjejeniya da gwamnatin tsohon shugaban kasar ta sanyawa hannu.

Wani babban janar din Amurka Joseph Dunford, wanda ya jagoranci rahoton, ya ce kungiyar Taliban na ci gaba da kai wa gwamnatin Afghanistan hari.

Yawancin masu s**ar shirin ficewar na fargabar maharan na iya kwace mulki da zarar sojojin kasashen waje sun fice.

Mutum 18 sun kammala digiri a gidajen yarin NajeriyaHukumar kula da gidajaen yari ta Najeriya ta ce ɗaurarru guda 18 ne ...
04/02/2021

Mutum 18 sun kammala digiri a gidajen yarin Najeriya

Hukumar kula da gidajaen yari ta Najeriya ta ce ɗaurarru guda 18 ne s**a kammala karatun digiri daga jami'ar karatu daga gida ta National Open University.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar mai suna Francis Enabore ya fitar a yau Alhamis ta ce tsararrun sun kammala jami'ar ne a fannoni daban-daban.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Mista John Mrabure yana taya su murnar kammala karatun sannan ya umarce su da su ɗauke shi a matsayin tubalin ginin rayuwarsu ta nan gaba.

"Kusan 'yan gidan yari 3,000 ne ke karatu a jami'ar Open University yanzu haka, yayin da 50 ke karatun shaidar koyarwa ta NCE a kwalejin Yewa da ke Jihar Ogun," a cewar Francis Enabore.

Ya ƙara da cewa hukumar na da cibiyoyin karatu guda 12 a gidajen yari da ke faɗin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa wani ɗan gidan yari ne ɗalibi mafi hazaƙa a jami'ar Open University a shekarar 2014 daga gidan yari na Jihar Enugu, inda wani ɗaurarren ya sake cimma wannan matsayi a 2018 da gidan

Sai nan da 2022 duniya za ta wartsake daga cutar korona - MDDAl'ummar duniya ba za ta wartsake ba "har sai nan da 2022",...
04/02/2021

Sai nan da 2022 duniya za ta wartsake daga cutar korona - MDD

Al'ummar duniya ba za ta wartsake ba "har sai nan da 2022", a cewar ɗaya daga cikin manyan likitocin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Farfesa Helen Rees, wadda ke cikin kwamitin MDD kan annobar cutar korona, ta ce rigakafin farko-farko na cutar ba zai yi tasiiri ba sosai a kan sabbin nau'in cutar.

Sak**akon haka ne, k**ar yadda ta shaifda wa BBC, tasiirin allurar rigakafin ba zai yi ƙarfi ba har sai nan da 2022.

Farfesar ta ce gwajin ƙarshe na rigakafin Novavax da Janssen ya nuna alamun nasara a kan sabon nau'in korona da aka samu a Afirka ta Kudu.

Sai dai ta ce masana kiwon lafiya na nuna damuwa kan rigakafin AstraZeneca da na Pfizer saboda sun yi amfani ne da ƙwayoyin cutar na asali daga China, yayin da ake kara samun sabbin nau'in nau'i a ƙasashe.

Buhari zai naɗa Buratai a matsayin jakada na musammanShugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aike da sunayen tsofaffin s...
04/02/2021

Buhari zai naɗa Buratai a matsayin jakada na musamman

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aike da sunayen tsofaffin shugabannin tsaro na ƙasar ga Majalisar Dattawa don amincewa da su a matsayin jakadu na musamman.

Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban, ya fitar ta ce Buhari ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan wasiƙa, inda yake neman amincewarsu.

"Bisa tanadin sashe na 171 (1) da (2) (c) da sakin layi na (4) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wanda aka yi wa kwaskwarima, ina mai neman amincewar Majalisar Dattawa don naɗa sunayen mutanen (5) da na lissafa a matsayin jakadu na musamman," in ji Buhari.

Waɗanda za a naɗa sun haɗa da: Janar Abayomi G. Olonisakin (mai ritaya) da Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) da Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) da Air Vice Marshal Mohammed S. Usman.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar ya nemi majalisar da ta gaggauta tabbatar da sojojin a kan matsayin nasu.

Mohammed S. Usman, shi kaɗai ne ba ya cikin manyan hafsoshin tsaron da Buhari ya sauke ranar Talata da ta wuce sannan ya maye gurbinsu da wasu domin ci gaba da jagorantar ayyukan tabbatar da tsaro a Najeriya.

Sabbin hafsoshin tsaron da aka naɗa su ne:

Janar Leo Irabor - Babban Hafsan Tsaro

Air-Vice Marshal I.O Amao - Babban Hafsan Sojan Sama.

Rear Admiral A.Z Gambo - Babban Hafsan Sojan Ruwa

Janar I. Attahiru - Babban Hafsan Sojan Ƙasa.

Mutum 6 sun mutu a wata gobara a AbujaA kalla mutum 6 ne s**a mutu a wata gobara da ta auku ranar Alhamis a kasuwar Tipp...
04/02/2021

Mutum 6 sun mutu a wata gobara a Abuja

A kalla mutum 6 ne s**a mutu a wata gobara da ta auku ranar Alhamis a kasuwar Tippe da ke 3rd Avenue a unguwar Gwarimpa a Abuja, k**ar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Rahotonya bayyana cewa mutane da yawa sun samu raunuka.

Wasu mazauna unguwar sun ce gobarar ta faru ne sanadiyyar wutar lantarki a wasu shaguna da misalin karfe sha biyu na dare.

An ruwaito cewa ta yi kusan awa biyu tana ci kafin jami'an kashe wuta s**a iso kuma a lokacin wutar ta riga ta yi nisa.

The Nation ta bayyana cewa wasu bata-gari sun yi amfani da wannan damar wajen sace kayan wasu shagunan.

Saudiyya ta rufe gidajen cin abinci da na kallo saboda koronaSaudiyya ta sanar da dakatar da harkokin nishadi da rufe gi...
04/02/2021

Saudiyya ta rufe gidajen cin abinci da na kallo saboda korona

Saudiyya ta sanar da dakatar da harkokin nishadi da rufe gidajen kallo da gidan cin abinci tsawon kwanaki 10, a wani mataki na daƙile cutar korona.

Ma'aiktar harkokin cikin gida ta ce adadin masu fama da cutar na ƙaruwa a kasar kuma tana ganin wannan matakin zai taimaka wajen hana cutar ci gaba da yaɗuwa.

An kuma dakatar da shagulgula ciki har da bikin aure da taruka tsawon kwana 30.

Kawo yanzu, mutum 369,000 ne s**a kamu da cutar korona a Saudiyya yayin da mutum 6, 400 s**a mutu. Ita ce kasar da ta fi ko wacce yawan mutanen da s**a mutu saboda cutar a kasashen yankin Gulf.

A jiya ne kasar ta ɗauki matakin rufe iyakokinta ga baki daga wasu ƙasashe 20 cikin har da Amurka da Masar da Lebanon da Turkiyya.

Ranar 17 ga watan Disamba ne Saudiyya ta kaddamar shirin riga-kafin korona bayan samo allurar daga Veserbiontech.

El-Rufa'i ya yi kira ga sauran gwamnoni da su yi tir da hare-haren ƙabilanciGwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wata sana...
04/02/2021

El-Rufa'i ya yi kira ga sauran gwamnoni da su yi tir da hare-haren ƙabilanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wata sanarwa da ke tir da wasu bidiyo da ake yadawa a shafuka sada zumunta mai nuna inda ake kashe ƴan wasu ƙabila da lalata gidaje a wasu sassan Najeriya.

Sanarwar mai dauke da sa hannun gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya ce yana takaicin mummunan tasirin da waɗannan hotunan za su yi musamman ga zaman lafiya kasar.

Ya kuma yi kira ga dukka ƴan Najeriya masu zama a jiharsa da su zama masu bin doka da kare hakkin abokan zamansu.

Gwamna El-Rufa'i ya ja hankalin takwarorinsa na sauran jihohi da su yi kira irin nasa sannan su yi alla-wadai da irin waɗannan hare-haren.

"Dole ne mu guji tashin hankali kuma mu zama masu bin dokoki a duk inda mu ke. Mun ga sharrin irin waɗannan hare-haren, wannna ya jawo abubuwa da dama k**a da karuwar aikta manyan laifuka da mace-mace," a cewarsa.

El-Rufa'i ya ce bai dace a ce ana ware ƴan wata kabila ko addini a laƙaba masu wani laifi ba.

"Shi ya a ma a jiharmu a shekrarar 2017 muka umarci k**a mutanen da s**a kori ƴan wasu kabila daga jiharmu," a cewar gwamnan.

Ya ce faragar da mutane ke ciki a fadin kasar nan saboda matsalolin tsaro, ya sa ya zama tilas shugabanni su dauki matakan hana aikata manyan laifuka da cin zarafin mutane.

Ya kuma yi kira ga 'yan majalisar dokokin Najeriya da su gaggauta sauya dokokin kundin tsarin mulki da za su samar da 'yan sanda jiha saboda a cewarsa wannan ne kawai zai tabbatar da bin doka a kasar baki daya.

Ya ce jiharsa ba za ta taba lamunta zargi ga mutanen da ba su ji b, ba su gani ba, ana dora masu laifukan da ba su aikata saboda kawai kasancewarsu 'yan wani bangare na Najeriya.

us: Saudiyya ta dakatar da ƴan wasu kasashe daga shiga ƙasarta Za a fara raba magunguna da jirgi marar matuƙi a KadunaGw...
03/02/2021

us: Saudiyya ta dakatar da ƴan wasu kasashe daga shiga ƙasarta

Za a fara raba magunguna da jirgi marar matuƙi a Kaduna

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar kaduna ya sanya hannu a wata yarjejeniya da wani kamfani mai suna Zipline kan wani tsari na raba magunguna a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar amfani da ƙananan jirage masu sarrafa kawunansu (drones).

Sanarwar da ta fito daga tawagar gwamnan ta yada labarai ta ce Gwamna El-Rufai ya ce wannan kamfani na Zipline na Kasar Amurka wanda ke da reshe a Ghana ya zabi Jihar Kaduna ne don ganin irin yadda jihar ta dauki sha’anin kiwon lafiya da muhimmanci.

Gwamnan ya kara da cewa, “ wannan tsari zai taimaka mana wurin rarraba magani da allurar riga-kafi zuwa duk lunguna da sakunan da ke jihar nan musamman inda muke fama da matsalolin tsaro k**ar Birnin Gwari da Chikun.

Haka kuma, ya ce jirgin na da firij wanda zai kare ingancin magungunan kafin su isa inda ya k**ata.

"Kuma za su rika isa inda ya k**ata cikin sauri a ko ina a fadin jihar Kaduna. Nan da ƙarshen watan Maris za a fara wannan tsari," a cewar El-Rufa'i.

Sannan wannan tsarin zai taimaka mana wurin samar da ayyukan yi ga matasanmu tunda a nan Kaduna za su rika kera wadannan jirage masu sarrafa kawunansu”, a cewar gwamnan.

Harin garin Sabuwa a jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar mutum 13An yi jana’izar wasu mutum 11 daga cikin 13 da ‘yan bin...
03/02/2021

Harin garin Sabuwa a jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar mutum 13

An yi jana’izar wasu mutum 11 daga cikin 13 da ‘yan bindiga s**a kashe a jiya Talata a garin Sabuwa da ke jihar Katsina.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun far wa duk wanda s**a yi tozali da shi ne a lokacin da s**a shigo garin da asubahin ranar Talata.

"Yara na dibar yashi a kan amalanken shanu lokacin da barayin dajin s**a shigo s**a ce su ba su shanun. Sai s**a ba su.

"Yaran sun dawo cikin gari s**a bayyana abin da ya faru to sai aka taru aka bi barayin aka je aka karbo shanun da s**a karba," a cewarsa.

Mutumin ya ce ashe barayin sun koma sun sanar da 'yan uwansu, nan da nan sai s**a dawo s**a far wa garin s**a k**a kashe mutane.

Ya ce barayin sun yi ayari ne a kan babura da yawansu ya kai dari s**a shigo garin dauke da mak**ai.

"Da s**a shigo sai s**a rarrabu, dama a baburan sun yi goyon mutum bibbiyu ne wasu kuma uku-uku. Wasu s**a nufi kasuwa s**a samu mutane s**a kashe a nan ma," in ji shi.

Ya ce jami'an tsaro ba su je inda tushen harin yake ba iyaka dai sun je kusa da garin amma babu wani mataki da ya ga an dauka.

‘Yan bindiga dai na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya, duk da ikrarin da hukumomi ke yi na kokarin shawo kan al’amarin.

Address

Niger State Kontagora
Minna
SENIORAGENTKYC

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aliyu Umar Dandalin labarai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share