Alhaji Musa communication Centre

Alhaji Musa communication Centre Selling phone and accessories

Yar uwa ki zama mai kamun kai ki rufawa kanki asiri, ki sani ba amfanin birgewar da bayan ta na dama ce, ki daina biyewa...
14/07/2023

Yar uwa ki zama mai kamun kai ki rufawa kanki asiri, ki sani ba amfanin birgewar da bayan ta na dama ce, ki daina biyewa Friends dinki a tiktok, Instagram, Facebook, Twitter, WhatsApp etc...

abinda k**e aikatawa da zasu ga yan uwansu mata na aikatawa da sun hukunta su domin su kare mutuncin yan uwansu, Ke kuwa ba abinda ya damesu dake domin ke ba kowa bace a wajansu, yar uwa ki kula da mutuncin ki, dana iya'yan ki, dana yaran da zaki haifa nan gaba ki daina biyewa son zuciya, ki tuna akwai ranar da ba'a dawo a gyara.😢

Allah ya tsaremana imaninmu da mutuncin mu baki daya.

Babu yadda za'a yi ki dinga siffanta kanki da shigar rashin da'a,amma ki nuna ke mutuniyar kirki ce, daga yanayin shigar...
14/07/2023

Babu yadda za'a yi ki dinga siffanta kanki da shigar rashin da'a,amma ki nuna ke mutuniyar kirki ce, daga yanayin shigar kamalan ki za'a iya fahimtar ki.

Ki ma daina yaudarar kanki da cewa, koda kinyi shigar da bai dace ba,amma ki ce imani a zuciya yake, tabbas an san imani a zuciya yake,amma kuma duk wanda zaiyi karo da irin shigar ki, abinda zai fara siffanta ki dashi, shine mutuniyar banza ce ke, saboda bakiyi shigar kamala ba.

Domin matan kirki,mata masu tarbiyya basa iya siffanta kan su da wani shiga daban wanda bana kamala ba,su kanyi shigar kamala ne daga dukkan suturan da suke sakawa,hakan ake son matan kirki su dinga siffanta shigar kamala a duk inda suke.

Bawai su zama matan dake bayyana surar jikin su ba,amma suna fakewa da Kalmar imani a zuciya yake,hakan tamkar isgili ne sukeyi wa Addinin musulinci, don Addini yayi umarni mata suke shigar kamala,suke siffanta kan su da shigar mutunci a duk in da suke.

Idan ma kina irin hakan lokaci bai kure miki ba,ki tuba ki daina irin wannan shigar.

Baka kyauta ba...Akwai mazajen da suke chatting a gaban matan su,basa kulawa da hakkin matar su sunfi mayar da hankali s...
14/07/2023

Baka kyauta ba...

Akwai mazajen da suke chatting a gaban matan su,basa kulawa da hakkin matar su sunfi mayar da hankali su wajen chatting zallah.

Ba'a hanaka karkayi chatting ba,amma kasan yadda zakana tafiyar da al'amuran ka,itama uwargidan ka bata hakkin ta,ka ware mata lokacin ta daban,wannan chatting din idan ta lura kafi mayar dashi akan kulawa da ita, za'a iya samun matsala saboda ba kowacce mace bace mai iya jurewa ko hakuri gaskiya,irin hakan zata haifar maku da matsala.

Wasu mazan da yawa sunfi mayar da hankali su wajen chatting zallah kawai,wani fa koda bama chatting din zaiyi ba amma wayarsa tafi masa,ya zauna suyi hira da matar sa bazai iya ba, gwanda yayi ta danne_danne a waya Kawai.

Gaskiya babu kyautatawa anan,ka gyara matar ka ta dinga samun lokacin ka fiye da lokacin wayar ka.

*Shawara ce*

FITINAR DA TA ƁULLO WA MATANMU A YAU!Ina farawa da sunan Allah Mai rahama Mai jin 'Kai. Dukkan yabo da godiya sun tabbat...
04/07/2023

FITINAR DA TA ƁULLO WA MATANMU A YAU!

Ina farawa da sunan Allah Mai rahama Mai jin 'Kai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki. Tsira da aminin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta (ﷺ).

Ya 'Yan uwana musulmi, na tsara zan yi wannan rubutu ne ba don komai ba sai don in ankarar da 'Yan uwa musamman mata da iyaye dangane da wata annoba ta lalacewa da ta tunkaro matanmu a yau.

A kokarin kafirai na ganin cewa sun bata tarbiyyar yaran musulmi, sun cire kunya daga jikinsu wadda aka san mata da ita a addinance da al'adance, da kuma kokarinsu na kawar da manufar aure tare da hana auratayyar gaba daya, sun kirkiro wadansu abubuwa (tools) wadanda Mace za ta iya amfani da su don biyan bukatarta (s*xual desires) ba tare da ta bukaci namiji ba. Hakika wannan haďarine mai girman gaske, kasancewar zai hana masu yin aure tare da cire masu kunya, kuma uwa ubama zai iya janyo masu matsaloli a jikinsu da kuma fushin Ubangiji.

Daga cikin waďannan abubuwa akwai abin da ake ce ma D***o, shi wannan wani abu ne wanda ake qera shi da roba (rubber) kuma a yi mashi kirar (shape) irin na al'aurar namiji, suna amfani da shi ta hanyar zura shi a gabansu, wanda su kan sanya wani mai (oil) wanda zai ba su damar shigar da shi cikin al'aurarsu, a haka za su yi ta yi har su gamsar da kansu (Cum/ejaculate).

Sannan akwai Vi****or, shi kuma wannan akwai wanda ake jona shi da wutar lantarki (electric), akwai kuma wanda ke amfani da battery (manual), suna amfani da shi ta hanyar wasa da al'aurarsu da shi (ma********on), shi ma dai idan mace ta yi amfani da shi tana samun gamsuwa ba tare da ta bukaci namiji ba. Na'udzubillah!

Akwai St***on, shi kuma wannan shi ma yana da kirar al'aurar namiji, Sannan akwai igiya a jikinshi kamar ďamara (belt), mace za ta daura shi a kugunta sai ta dinga yi wa wata macen irin yadda namiji ke yi wa Mace. Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un!

Akwai sauran S*x toys kala-kala wanda duk an yi su ne saboda wannan manufar. Kuma mafi yawa daga ciki 'yan madigo (le****ns) ne suke amfani da su.

Asali wadannan abubuwa ana amfani da su ne a kasashen yammaci, wato yankin turawa kenan, amma a yanzu na samu labarin cewa wasu gur6atattu a nan kasar (Nigeria) sun fara yo safararsu (ordering) daga kasashen ketare zuwa wannan kasa tamu mai albarka, kuma ma har ya shigo yankin mu na arewa wanda yanki ne na musulmi, da kunnena na ji wata tana ikirarin cewa ta kusa fara yin safarar irin wadannan kayayyaki tunda ta fahimci cewa mazan hausawa ba su iya biya wa matansu bukata ba (Kun ji karya!), wannan abu ya tada min da hankali matuka, shiyasa na za6i in yi wannan rubutu don farkar da 'Yan uwa game da muni da illar wadannan abubuwa.

Amfani da irin wadannan abubuwa be tsaya a kan 'Yan mata kaďai ba, da yawa a kan samu Zawarawa da Matan aure ma suna amfani da shi, musamman matan da mazansu ba su iya gamsar da su. Dayawa mata suna daukar wannan dabi'ar ne daga lalatattun Qawaye a gida ko a makaranta, ko ta hanyar shiga dandali (groups/pages) na 'yan maďigo da labaran batsa a yanar gizo, ko ta hanyar kallace-kallace na fina-finan nuna tsiraici (pornographic videos), da cakuduwa da matan Banza.

*ILLOLIN IRIN WADANNAN ABUBUWA.*

—Yin amfani da wadannan abubuwa haramun ne, kasancewar ya sa6a wa hanyar da shari'a ta taskance don biyan bukata, wato *aure* tsakanin mace da namiji.

—Sannan wannan abune da zai iya barazana ga lafiyar mace, kasancewar tana shigar da wani abu jikinta sa6anin wanda aka yi gurin don shi.

—Yin amfani da su yana zubar wa mace da budurcinta tun kafin ta yi aure, wannan zai iya sa koda ta yi aure mijinta ya sake ta ko zargi ya shiga tsakaninsu domin ba ta da wani bambanci da bazawara. Kasancewar tsokar da ke rufe da farjinta (h***n) wanda ke da alaka da budurci (chastity/virginity) zai fita daga lokacin da ta fara amfani da irin wadancan abubuwan.

—Yana cire wa mace son aure gaba daya, sai ka ga mace ta manyanta amma ko maganar aure ba ta yi, domin a nata tunanin ai tana samun duk abin da za ta iya nema daga namiji.

—Ga matar aure, zai cire mata sha'awar mijinta, domin za ta ji ba ta iya samun gamsuwa daga mijinta har sai ta yi wancan abin da ta saba.

—Yana janyowa matsala daga kwakwalwa kamar yawan mantuwa, kasancewar akwai ragowar ruwa (s*x fluid) wanda ba ya samun fita sai ta hanyar saduwa da namiji, to wannan ragowar yana komawa ya shafi (affecting) din kwakwalwarta (Central Nervour System).

—Baqaqen aljanu (Jinnul ashiq) za su iya shiga jikinta a lokacin da take wannan abin, kuma za su janyo mata matsaloli masu girma a rayuwarta, ko dai su aure ta su hana ta aure da dan adam, ko kuma ko ta yi auren ta ki samun haihuwa ko kwanciyar hankali.

Wadannan wasu kenan daga cikin illolin wadannan abubuwa.

*HANYOYIN MAGANCE WANNAN MATSALA*

—Wajibi ne Iyaye su sa ido sosai a kan kaiwa da komowar yaransu, su san abin da suke yi idan sun kaďaitu a ďaki, su dinga yawan duba (searching) na jakarsu domin mafi yawan 'yan mata masu yin wannan yawo da shi a jaka.

Sannan Uwa ta dinga kokari wajen nuna wa 'yarta darajarta da abin da zai kai ga zubar mata da kimarta tare da kai ta ga fada wa cikin fushin Ubangiji.

Uwa ta koya wa 'yarta ayyukan cikin gida domin ta shagaltar da ita da aikace-aikace, wannan zai sa sha'awa ba za ta dinga mata barazana ba.

—Iyaye su ji tsoron Allah su dinga aurar da yaransu daga lokacin da s**a balaga matukar sun samu manemi. Kada a bijiro da wani al'amarin duniya kamar gama karatu d.s.

Mazan da ba su iya gamsar da iyalinsu sakamakon wata lalura su ji tsoron Allah su nemi magani.

—Ki kare idanunki daga kallace-kallacen videos da pics na tsiraici ko karatun littafai na batsa.

—Ki Shagaltu da ambaton Allah, karatun Alqur'ani da salloli na nafila da azumin nafila.

Sannan daga karshe ina shawartar hukuma da masu fadi a ji da su sa ido a kan masu shigo da irin wadannan kayayyaki, fasa kauri (smuggling) na shinkafa da makamai ba shi kadai bane matsalarmu, makomar tarbiyyar 'ya'yanmu ma abin dubawa ce.

Ya Allah Ka shiryar da mu.

✍🏿Ayyub Musa Giwa.
(Abul Husnain).

Daga Zauren
*📚 Irshadul Ummah.*

Ku yi sharing don wasu su amfana ta sanadiyarka!

27/08/2022

Address

Lagos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alhaji Musa communication Centre posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Alhaji Musa communication Centre:

Share