Amis online comm

17/08/2026
Gidaje biyar (5) ba'a auren Yar su kuma a Zauna lafiya Wani lokacin…kuskuren da muke yi a aure baya farawa daga wajen ma...
17/07/2026

Gidaje biyar (5) ba'a auren Yar su kuma a Zauna lafiya
Wani lokacin…
kuskuren da muke yi a aure baya farawa daga wajen macen.
Yana farawa ne daga kofar gidan da muka je neman aurenta.

​Na taba tunanin cewa soyayya zata iya goge asalin tarbiyyar da mutum ya taso da ita. Kuskure na ne. Idan ka duba gida ko iyaye, akwai irin gidajen da koda yarinyar tana matukar son ka, dabi'ar gidansu zata rushe maka natsuwa a hankali. Ga gidaje biyar da auren 'yarsu siyan kuncin zuciya ne:

1. ​Gidan Auna Daraja Da Kudi: Gidan da iyayenta suke lissafin kaurin aljihunka kafin su kalli mutuncinka. Idan ka taba faduwa a kasuwa gobe, yarinyar ba zata taba yi maka uzuri ba, domin a asalin gidansu, kudi ne kadai yake bayar da darajar 'Da Namiji.

2. ​Gidan Murkushe Da Namiji: Idan ka lura cewa a gidan, mahaifinta bashi da fada aji, kuma mahaifiyarta ita take yanke kowane hukunci. Ka kiyaye. Ba zata taba baka girman miji ba, domin bata taba ganin mahaifiyarta tana bawa mahaifinta ba.

3. ​Gidan Gasa Da Fariya: Gidan da kowa yake rayuwa don ya burge wani. Zata shigo gidanka tana kallon irin dinkin da kawayenta ko 'yan uwanta suke yi. Zata matsa maka sai ka ci bashi ko ka fasa asirinka don kawai ta yi gaba da su.

4. ​Gidan Rashin Sirri: Gidan da babu asiri a cikinsa. Duk abin da ya faru tsakaninka da ita a daki, koda na kuskure ne, washegari zai zama labarin dangi. Ba zaka taba samun kwanciyar hankali ba idan kana zama da macen da take tallata rauninka a waje.

5. ​Gidan Daurewa Kuskure Gindi: Gidan da idan yarinyar ta yi maka ba daidai ba ka kai kara, maimakon iyayenta su tsawatar mata, sai su nuna kai ne mai laifi ko su shiga gabanta. Zaka zauna da macen da bata taba jin tsoron bacin ranka ba.

​Aure ba hada jiki bane kawai.
Hada asali ne.
Kuma wani asalin… guba ne.

kadijah adamu gone
Amis online bd I T channel

Data sharing ontop ne.Allah Ne Ya tsaremu A cikin Ikonsa.....Bawai Zan Nemi a tausayamin bane Ko a sassautamin, Bana Buk...
16/07/2026

Data sharing ontop ne.Allah Ne Ya tsaremu A cikin Ikonsa.....

Bawai Zan Nemi a tausayamin bane Ko a sassautamin, Bana Bukatar Sassaucin kowa saina Mahaliccina Duk wani Hali da muka tsinci kanmu a wannan tsari na gwagwarmaya Muna cigaba da godewa Allah ne.

Wannnan Shine Zuwa Kotunmu Na 23 kenan a tsowon watanni bakwai 7 da muka shafe muna fuskantar wannan case din Kullum Indai kotu zata nememu haka muke bin wannann hanya mai dauke da ƙalubale daga kano zuwa FCT Abuja.

Ba wani Abu da muke bukata a wajenku Alummah sai addu’a saboda itace makamin muminai,mudai bamu da tsumi bamu da dabara mun barwa allah komai yayi yadda yaso damu a cikin ikonsa.

Sanata shehu buba mai wakiltar bauchi south kuma wanda yake neman takarar Gomna a jihar ta Bauchi a jam’iyyar PRP Shine wanda ya shigar damu Wannan ƙara a federal high court dake Mai tama a abuja.

Allah ya kara kiyaye mu baki allah ya dora Gaskiya akan ƙarya.

Amis online bd I T channel

15/07/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Amila Ramanayaka, Pubg Real

08/07/2026

TikTok | Make Your Day

Saqon Ali Rabiu ali, Rarara ya ce wajibine duk dan kannywood ya tallata Tinubu, kuma Umarni ne. To mutane na tabayata as...
06/07/2026

Saqon Ali Rabiu ali, Rarara ya ce wajibine duk dan kannywood ya tallata Tinubu, kuma Umarni ne. To mutane na tabayata ashe dole sai mun yi kenan?
Amsa: Mahaifina ya rasu Allah Ya jikansa da Rahma, shi ne kadai zai min Umarni na bi akan wani abu, kuma dole na yi domin a tarbiyyar Addinin musulunci "Biyayya ga iyaye wajibine, ko da kuwa za ka yi tallan gumakan Annabi Ibrahim ne"' to amma fa duk musulmin kwarai ya san Umarnin musulunci akan cewa: "Babu bi ga abin halitta gurin sabawa Mahalicci"
Don haka babu ni a ciki. Allah Ya kawo mana karshen zalinci.
Ali Rabi'u Ali

Amis online comm

Bauchi: An Yi Fatali Da Buƙatar 'Yan Tijjaniyya Na Neman Gina Masallaci A Jami'ar ATBU Hukumar Gudanarwar Jami'ar Abubak...
01/07/2026

Bauchi: An Yi Fatali Da Buƙatar 'Yan Tijjaniyya Na Neman Gina Masallaci A Jami'ar ATBU

Hukumar Gudanarwar Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi, ta sanar da soke shirin bai wa ƙungiyar ɗaliban ɗarikar Tijjaniyya fili a harabar jami'ar, tare da umartar dukkannin mabiya ɗariku da sauran al'ummar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadunsu a babban Masallacin jami'ar ba tare da wata tsangwama ba.

Wannan na zuwa ne bayan Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na jami'ar, Malam Zailani Bappa, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar kamar yadda Albarka Radio ta rawaito.

A cewarsa, an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da jami'ar ta yi da jami'an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da kuma sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jami'ar.

K@inuw@

01/07/2026

CIKAKKEN BAYANI KAN KISAN MALAM AMARABAR JOS.

30/06/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Ibrahim Ashafa Yakasai, Mohammed Jamil, Zainab Yusuf, Yusuf Sharif Abdullah, Bello Yunusa, Alley Jabir Binya, Oumarou Abdourahamane, Ibrahim B Shuaibu Zaria, Usman Ahmad Dutse, Titus Sani, Abdouraman Mohammadou, Sa'ad Musa, Amos Manasseh, Musa Yohanna, Mohammed Garba Wakil, Inssasoumana Hassan, Mouss Labo Mahaman Rabilou, Aliyu Umar, Mustapha Muhammad, Mohamadou Mohamadou, Samira Usman, Abdallah Jibril Muh'd, Alhaji Bukar Mala, Umar Lawal, Michael B. Ojo, Abubakar Ayuba, Sumaina Jay Omoh, Fatima Shehu, Hassan Ahmad Auyo, Zurkallaini Akiri, Saminu Tungar Haki, Adamu Mohammed, Brittany Hackett, Aliyu Wazziri, Hassan Sharif, Olaoluwa Ifeoluwa, Musa Adam, Mohammad Masoyi Muhammad Masoyi, Mohammed Yusuf, Almussafa Dan Gsk, Shuaibu Gambo, Yusif A Loko, Kabeer Hamxa, Mohammed Abubakar, Moudansir Laminou, Aliyu Saleh Aliyu, Bashir B Dala, Salisu Rabi'u, Muntari Loki, Sabiha Mahamadou Dakaré

Babbar kotun tarayya mai lamba 1 da ke zama a Gombe ta fara sauraron ƙaran da aka shigar kan takarar Farfesa Isa Ali Ibr...
29/06/2026

Babbar kotun tarayya mai lamba 1 da ke zama a Gombe ta fara sauraron ƙaran da aka shigar kan takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a jam'iyyar PDP.

An shigar da karar ta hannun Abdulkadir Hamma Saleh, wanda ke ƙalubalantar zaman Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Gombe.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026 cewa shari'ar ta zo gaban mai shari'a, Amina Aliyu Mohammed

Alkalin kotun ta ɗage zaman kotun har zuwa ranar 9 ga Yuli, 2026, domin ci gaba da sauraron karar.

Amis online bd I T channel

Sahala media tv

Address

Awe Street Sabon Pegi
Lafia

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amis online comm posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Amis online comm:

Shortcuts

Share