Combat Computer Technology

Combat Computer Technology Computer training, business center and consultancy services

02/01/2025

ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR [ALHAMIS]

NASIHAR'MU TA YAU
Duk ƙofar da ka ganta a rufe tabbas tana da mabudi, kada ka saki baki kana jiran tabude da kanta, haka komai da ka sani a duniya yana da mabudi, mabudin ilmi shine tambaya, Mabudin nasara shine haƙuri, mabudin arziki tsoran Allah, Mabudin zaman lafiya adalci da gakiya.

Mu yawaita Addu'a da istigfari Allah ya ƙaro mana arziki da sauƙin rayuwa Ameen ya Allahu

12/10/2022

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (11)
**********
Da Sunan Allah Rayayyen Sarkin da gyangyadi bai ta'ba riskarsa ba, b***e barci. Salati da aminci su tabbata bisa Ma'abocin Farkon Zance aranar da dukiya da 'ya'ya basu amfani, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Gwargwadon girmansa.

Hakika lamarin Alqiyamah da girma yake.. Babu mai tsallake firgicinta sai wadanda Allah ya za'ba daga cikin bayinsa.

Yayin da Mala'ika Israfeelu yayi busar farko acikin Qaho, dukkan mutane basu firgita su dimauce da eehu tamkar mashayan dake tambele. Kuma wannan firgitar da tashin hankalin da sumewar bata kebanci 'yan Adam kadai ba. Domin kuwa Allah cewa yayi :

"RANAR DA ZA'AYI BUSA ACIKIN QAHO SAI DUKKAN WADANDA KE CIKIN SAMMAI DA WADANDA KE CIKIN QASSAI SU FIRGICE, SAI DAI WADANDA ALLAH YASO... "

Wato wannan firgitar zata shafi kowa da kowa. Daga nan sai kuma mutuwa ta riskesu baki daya.

Ibnu Hajr Al Asqalaniy (rah) yace "Busa ne guda biyu - ta farkon acikinta ne duk masu mutuwa zasu mutu. Wadanda Allah ya kebancesu kuma zasu suma. Idan anyi busar Qaho ta biyu kuma acikinta ne kowanne matacce zai tashi, Kuma kowanne sumamme zai farfado".

Ubangiji ya buga misali da Jarirai har sau uku game da girman tashin hankalin Alqiyamah. Ya siffata mana ita k**ar haka :

- Ranar da zaku ganta, Kowacce mai shayarwa zata jefar da abinda take shayarwa.

- Ranar da Mai ciki zata haife abinda take dauke dashi.

- Ranar dake sanya jarirai yin furfura.

Duk wanda yake so yaga yadda Alqiyamah zata kasance k**ar akan idonsa, to ya karanta surorin nan guda uku :

- Idhash Shamsu kuwwirat. (Suratut Takweer).

- Idhas Sama'un Fatarat (Suratul Infitaar).

- Idhas Sama'un Shaqqat (Suratul Inshiqaq).

Abubuwan dake gabanmu yanzu anan duniya sune k**ar haka :

- Sararin samaniya.
- Qasa.
- Duwatsu.
- Tekuna.
- Dabbobi.
- Rana, Wata da Turari.

To dukkan wadannan abubuwan Allah ya bamu labarin yadda makomarsu zata kasance aranar Alqiyamah.

SAMMAI : Allah yace "Idan sama aka kyeceta".

QASSAI : "Idan aka girgiza Qasa mutukar girgizawarta, Kuma Qasa ta fitar da nauye-nauyenta".

DUWATSU : "Ranar da za'a nike Qasa da duwatsu".

"Kuma duwatsu zasu zamanto tamkar gashin buzun da aka jeme".

TEKU : Allah yace "Kuma idan tekuna s**a kyakkece (S**a hade da junansu).

"Idan tekuna aka cinna wuta garesu".

Wato zasu hade da junansu kuma daga karshe Ubangiji zai sa su k**a da wuta baki dayansu.. (SUBHANALLAH).

DABBOBI : "Idan dabbobi aka tashesu (Domin yin hisabi atsakaninsu)

RANA DA TAURARI : "Idan rana aka tafiyar da haskenta, Idan Taurari aka gurbacesu (wato launinsu ya chanza, s**a gauraye da junansu).

Ibnu Abi Hatam ya ruwaito hadisi ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) yana cewa "Rana da Wata da Taurari Allah zai dulmiyar dasu acikin Teku ne aranar Alqiyamah sannan ya aiko da wata iska mai Qarfi wacce zata cinna musu wuta".

Wannan kenan daga abubuwan da duk wani mai rai awannan lokacin sai ya gani da idonsa idan lokaci yayi.

Ya Allah kasa mu cika da imani ameen.

25/09/2022
MAI'ADUA MUNA MAKU BARKA DA SHANRUWA
26/04/2022

MAI'ADUA MUNA MAKU BARKA DA SHANRUWA

GOOOD BYE   L.G.ACikin ikon Allah yau Lahadi 6/3/2022 mun kammala program dinmu na computer training a cikin karamar huk...
06/03/2022

GOOOD BYE L.G.A

Cikin ikon Allah yau Lahadi 6/3/2022 mun kammala program dinmu na computer training a cikin karamar hukumar Kurfi wanda ma'aikata, matasa da dalibai s**a amfana da wannan karatu da akayi.

Muma godiya ga Allah daya bamu rai, lafiya da lokacin da muka dauka domin bada wannan gudunmuwa ta ilmantar da al'umma wannan ilimi.

Godiya ta musamman ga abokan aiki Muhammad Nafi'u Yahaya da Nazifi Isah Garia tare da Financial secretary na wannan group wato Bishir Suleiman Kurfi, Kurfi local government coordinator Sani Umar da takwaranshi na Dutsinma Ibrahem Shehu Abu Hajarah, NUT chairman da dukkan wadanda s**a bada gudunmuwa ta shawarwari, lokaci da sauransu don ganin an samu nasarar tafiyar da wannan program.

Muna rokon Allah yasa wannan karatun ya zama mai albatka da alheri garesu da al'umma baki daya.

DAY 1 MAI'ADUA LOCAL GOVT. Yau 1/3/2022 cikin ikon Allah gamu a garin Mai'adua a rana ta farko domin fara computer liter...
01/03/2022

DAY 1
MAI'ADUA LOCAL GOVT.

Yau 1/3/2022 cikin ikon Allah gamu a garin Mai'adua a rana ta farko domin fara computer literacy training wadanda ma'aikata, dalibai da matasa zasu amfana da wannan shirin.

Wannan program na tafiya karkashin jagorancin training manager Mal. Nafiu, local government coordinator Mal. Zakari tare da mataimakinsa Mal. Zaruku Ahmad da kuma kulawar NUT Chairman Mal. Salmanu Abba.

01/03/2022

DAY 1
MAI'ADUA LOCAL GOVT.

Yau 1/3/2023 cikin ikon Allah gamu a garin Mai'adua a rana ta farko domin fara computer literacy training wadanda ma'aikata, dalibai da matasa zasu amfana da wannan shirin.

Wannan program na tafiya karkashin jagorancin training manager Mal. Nafiu, local government coordinator Mal. Zakari tare da mataimakinsa Mal. Zaruku Ahmad da kuma kulawar NUT Chairman Mal. Salmanu Abba.

KURFI
25/02/2022

KURFI

GOOD BYE TO UNGUWAR GARIYA, YARI-BORI ZONE, KAFUR LGAA yau cikin ikon Allah mun kawo karshen computer literacy training ...
13/02/2022

GOOD BYE TO UNGUWAR GARIYA, YARI-BORI ZONE, KAFUR LGA

A yau cikin ikon Allah mun kawo karshen computer literacy training da muka dauki mako biyu muna gudanarwa a garin Unguwar Gariya dake yankin Yaribori ta karamar hukumar Kafur.

Manufar wannan program shine domin matasa, dalibai da ma'aikata su samu wannan ilimi na na'ura mai kwakwalwa a saukake kasancewa ilimin computer ya zama ruwan dare kuma abinda akeso a samu domin samun saukin aiki a kowane bangare.

Bayan godiya ga Allah daya bamu ikon farawa da kammalawa lami lafiya, muna kuma kara godiya da jinjina ga babban malaminmu Mal. Muhammad Nafi'u Yahaya da kuma wadanda s**a jagoranci wannan training kuma masu masaukin baki wato Mal. Aminu Isah Gariya, Mal. Nazifi Isah Garia, Mal. Mansur Ibrahim Gariya da dai sauran dukkan wadanda s**a bada gudunmuwa don ganin an samu nasarar tafiyar da wannan karatu. Muna godiya sosai tare da fatan Allah ya bamu ladan dake cikin yada ilmin garemu baki daya.

Muna rokon Allah yasa albarka a cikin karatun, ya amfanesu da sauran al'umma baki daya.

Combat CT
2022.

RANA TA 6 A GARIN U/GARIYA, KAFUR LGACOMPUTER LITERACY TRAINING
02/02/2022

RANA TA 6 A GARIN U/GARIYA, KAFUR LGA

COMPUTER LITERACY TRAINING

RANA TA UKKU A GARIN UNGUWAR GARIYA DAKE YANKIN YARIBORI, KARAMAR HUKUMAR KAFUR.MATASA, MA'AIKATA DA DALIBAI NE KE KOKAR...
30/01/2022

RANA TA UKKU A GARIN UNGUWAR GARIYA DAKE YANKIN YARIBORI, KARAMAR HUKUMAR KAFUR.

MATASA, MA'AIKATA DA DALIBAI NE KE KOKARIN KOYON YADDA ZASU SARRAFA COMPUTER.

DAY 2 @ UNGUWAR GARIYA CENTER, KAFUR L.G.A Computer Literacy Training
29/01/2022

DAY 2 @ UNGUWAR GARIYA CENTER, KAFUR L.G.A

Computer Literacy Training

Address

Katsina

Telephone

+2347067704040

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Combat Computer Technology posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Combat Computer Technology:

Share