26/11/2022
The Reality Of Cryptocurrency
Yaudara da propaganda ita tafi yawa fiye da komai a kasuwar crypto, bibiyar kasuwar da kasancewa updated akanta koyaushe tare da neman ilimi shine zai bude maka ido a kasuwar. Duk project daka gani na crypto suna tabbatar da sunyi manipulating na tunanin community kafin a rubuta Whitepaper.
Daga lokacin da ka fahimci cewar a kasuwar crypto, babu wani mai mallakar wani project da zai fito ya fada maka gaskiya, toh ka huta. Muna magana da Oga Sunusi yake ce mini:- Kaga Muhammad wallahi duk crypto dinan da kake gani social media hype ne kawai dss.
Akwai course da nayi certificate akan shi Social Engineering, karatu ne mai dadi sosai, sannan yana da matuqar.... Hmmm😎. Cikin sa akwai wani fanni da ake kwarewa akwai wanda nima nayi sa, ana kiran abinda suna SWOT ANALYSIS (Strengths/Weaknesses/Opportunities/Threats).
Na rantse da As-samadu idan mutum yayi Social engineering kuma yayi karfi akan SWOT da sauran fannuka masu mahimmanci a Psychology, to babu kwakwalwar da bazai iya manipulating ba. Manyan yan kasuwa, yan siyasa da Tech Companies sunaa da masu musu irin wannan tunanin.
Za'a fito a fada maka karya, kuma na rantse da Allah zaka iya rantsuwa akan cewa gaskiya ne. Baka mamakin yadda ake rubuta whitepaper ne? Cikakkiyar whitepaper fa kaso 5% ne ake fada maka sirrin project, 95% hype ne da karairayi. Amma kai kace gaskiya ne.
Shiyasa sanin yadda abin yake tafiya ba alfahari ba ina karanta whitepaper nake iya fahimtar abinda masu project suke kokarin boyewa. Da zarar na karanta whitepaper na project shikenan kawai, shiyasa neman ilimi a kowacce sana'a yake da muhimmanci.
Shiyasa da zarar naga mutum yana hakikicewa akan wani project bama iya na crypto ba kowanne me, sai kawai nayi dariya nace an ci shi da yaki. Da zarar kayiwa abin kololuwar fahimta zaka gane nothing have ever done for your own benefit. It's just about capitalism.
Author: Muhammad Abdulrahman Sheka
(Gobe ranar 27th Nov 2022 zan cika shekara daya cif da fara bayar da ilimi akan harkar crypto)
Telecommunication company