HausaStack

HausaStack Hausa Programmers wani group ne a Nigeria Wanda zasu rinka koyardaku yadda ake programming da harshen hausa

Hausa Stack is a technology learning platform created to make tech education simple, clear, and accessible to Hausa speakers. We focus on teaching programming, CMS platforms like WordPress, website design and development, domain registration, hosting, SEO, and many other digital skills in a step-by-step way. Our goal is to help beginners and learners build real tech skills, grow their knowledge, a

nd create opportunities in the digital world. All lessons are explained in simple Hausa language to remove language barriers and make learning easier for everyone. Follow Hausa Stack to learn coding, build websites, manage online tools, and grow your digital skills with clear and practical tutorials.

🌐 Menene DNS? | What is DNS?DNS (Domain Name System) wani tsarin internet ne da yake taimakawa wajen juya sunan website ...
31/12/2025

🌐 Menene DNS? | What is DNS?
DNS (Domain Name System) wani tsarin internet ne da yake taimakawa wajen juya sunan website zuwa IP address. Mutane suna amfani da sunaye kamar www.example.com, amma computers da servers suna fahimtar numbers (IP addresses).

DNS yana aiki ne kamar littafin waya (phonebook) na internet. Idan ka rubuta sunan website a browser, DNS ne ke taimakawa wajen nemo inda server ɗin website take, sannan ya haɗa ka da ita cikin sauri.

Misali:
Idan ka rubuta www.example.com, DNS ne ke gano ainihin adireshin IP dinda ke ɗauke da wannan shafin – kamar 12.34.56.78 – wanda kwamfutarka ke buƙata domin ta san inda zata nufa.

Kamar yadda zaka iya rubuta sunan abokinka a waya maimakon tuna lambar sa, haka DNS ke sauƙaƙa mana wajen shiga shafukan yanar gizo wato (Websites).

⚙️ 4 Features na DNS
1️⃣ Name Resolution
DNS yana canza domain name kamar www.example.com zuwa IP address da computer zata iya fahimta.
👉 This makes websites easy to remember.

2️⃣ Speed & Performance
DNS yana taimakawa wajen saurin buɗe websites ta hanyar caching.
👉 Faster loading time for users.

3️⃣ Reliability
DNS servers suna da yawa (distributed). Idan ɗaya ta bar aiki, wata zata yi aiki.
👉 This keeps the internet running all the time.

4️⃣ Security Support
DNS yana taimakawa wajen tsare website, kamar blocking din malicious domains da phishing sites.
👉 Helps improve network security.

Mecece Computer? Bayani Cikin Sauki a HausaWannan bidiyon zai taimaka maka ka fahimci mecece kwamfuta. Munyi bayanin kom...
10/10/2025

Mecece Computer? Bayani Cikin Sauki a Hausa
Wannan bidiyon zai taimaka maka ka fahimci mecece kwamfuta. Munyi bayanin komai a cikin harshen Hausa. Idan kai sabo ne wajen amfani da kwamfuta, Wannan bidiyon naka ne. Za ka san ma’anar kwamfuta, Yadda kwamfuta take aiki, da kuma muhimmancinta. Munyi wannan bidiyon ne da yaren Hausa domin sauƙaƙa maka wajen fahimtar ta, Wannan shi ne mataki na farko wajen sanin mecece computer.



Wannan bidiyon zai taimaka maka ka fahimci mecece kwamfuta. Munyi bayanin komai a cikin harshen Hausa. Idan kai sabo ne wajen amfani da kwamfuta, Wannan bidi...

Address

Abuja
900108

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HausaStack posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HausaStack:

Share