16/10/2025
DIGITAL TECHNOLOGY
Ita dai Fasahar zamani (Digital Technology) ita ce fasaha da ake amfani da ita wajen samar da sabbin abubuwa, adanawa, da sarrafa bayanai cikin tsarin lambobi biyu — 0 and 1. Wannan ya bambanta da fasahar analog wadda ke amfani da siginal (continuous signals). Fasahar dijital tana ba da damar aiki cikin sauri, adana abubuwa cikin sauƙi, da samun sakamako mai inganci.
A yau, fasahar dijital tana taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum daga wayoyin salula, kwamfutoci, da intanet, zuwa fasahar wucin gadi (AI), ajiyar bayanai a sararin sama (cloud computing), da kafofin sada zumunta.
Misalan fasahar dijital sun haɗa da:
Kwamfutoci da wayoyin hannu
Hanyoyin sadarwa na dijital (misali imel, WhatsApp, da Facebook da sauran su)
Intanet da hanyoyin sadarwa
Fasahar wucin gadi (AI) da koyon na’ura (Machine Learning)
Ajiya da sarrafa bayanai a sararin samaniya
Na’urori masu aiki ta atomatik da robot.
Barkaku da wowa
Muhimmancin fasahar dijital:
Sauƙaƙe sadarwa:Ta na ba da damar yin magana ko aika saƙo cikin ɗan lokaci daga ko’ina cikin duniya.
Ƙara yawan aiki: Aiki yana tafiya cikin sauri ta amfani da kwamfuta da na’urorin dijital.
Samun bayanai cikin sauƙi: Intanet na ba da dama ga ilimi, bincike, da nishaɗi.
Ƙarfafa kirkire-kirkire: Tana taimakawa wajen ƙirƙira, zane-zane, da wallafa abubuwa.
Ƙarfafa tattalin arziki: Tana taimaka wa kasuwanci da kirkirar sabbin hanyoyin samun kuɗi.
A taƙaice, fasahar dijital ta sauya yadda mutane ke rayuwa, aiki, da sadarwa, tana mai da duniya wuri mai haɗuwa da saurin ci gaba.