Smartdata4u

Smartdata4u We offer instant recharge of Airtime, Databundle, CableTV (DStv, GOtv & Startimes), Electricity Bill Payment and more

12/10/2026

Dan uwa, wallahi billahi da za ka shiga kabari ka ga yadda ake kwanciya a can, da duk duniyar nan ta zama wulakantacce a idonka.

Mutuwa bata da rana. Bata da shekaru. Bata tambayar ka "Shin ka shirya?"

Jiya da yamma wani yana cikinmu, yanzu yana karkashin kasa. Ana ta maganar "Allah ya jikansa" a kansa.

Ka tambayi kanka yau:

Idan Mala'ikul Mauti ya zo maka yanzu, a wannan mintin, me ka tanada?

- Wayarka cike da hotunan haram da wakoki?
- Zuciyarka cike da hassada da gaba da mutane?
- Sallarka tana biye maka ko tana binsa?

Wallahi kabari akwati ne. Kowa zai shiga shi shi kadai. Babu uwa, babu uba, babu mata, babu kudi. Sai aikin ka.

Annabi SAW yace: "Ku yawaita tuna mai yanke dadi (wato mutuwa)."

Domin duk wanda ya yawaita tunawa da mutuwa, zai yi watsi da duniya, zai yafewa mutane, zai rike sallah.

Dan uwa / 'Yar uwa...

Wannan Lokacin da kake a kwance, ka tabbatar zaka tashi ?

Idan baka tabbatar ba, to me yasa baka tuba ba yanzu?

Tashi ka yi alwala. Ka yi raka'a biyu. Ka ce: "Ya Allah, ka yafe min. Na dawo gare ka."

Kada ka bari mutuwa ta riske ka kana cikin sabo. Kada mutane su bude wayarka bayan mutuwarka su ga abin da zai kunyata ka a kabarinka.

Mutuwa na kusa. Kusa da yawa fiye da yadda kake tunani.

Allah Ya sa mu cika da imani.

Ka tura wa wani, watakila zuciyarsa ta Tuna Mutuwa sanadin Ka

Allah yasa mu dace

11/10/2026

SALLAR DARE💚
Allah baka iko

09/10/2026
26/09/2026

KARKA WANI DAMU, DON ALLAH YA JARABCE KA DA CUTA, GORMA KA MUTU DA KA JE WAJEN BOKA.

Ya dan uwana mai ciwo, mai fama da radadi, mai kwance a asibiti ko a gida.

Ka sani, cutar da kake fama da ita yanzu, ba tsinuwa bace. Jarrabawa ce. Kuma jarrabawa daga Allah rahama ce, ba fushi ba.

Allah bai jarabce ka ba saboda Ya ki ka. A'a, Ya jarabce ka ne saboda Yana son ka. Yana son Ya ji kukan ka. Yana son Ya goge maka zunubanka. Yana son Ya daga darajarka.

KA DAU DARASI DAGA ANNABI AYYUB (A.S)

Annabi Ayyub, Annabin Allah, bawan Allah na gari.

Allah Ya ba shi dukiya, Ya ba shi 'ya'ya 10, Ya ba shi lafiya. Sannan sai Allah Ya jarabce shi.

A rana daya, dukiyarsa ta tafi.
A rana daya, 'ya'yansa 10 s**a mutu gaba daya.
Sannan jikinsa ya fara ciwo.

Cutar da ta fi kowace cuta muni. Shekaru 18 yana fama.

Jikinsa ya rube, tsutsotsi na fita daga jikinsa, mutane s**a daina zuwa wajensa, s**a kore shi daga birni, ya koma daji.

Matarsa daya ce kawai ta rage a wajensa, tana aiki tana ciyar da shi.

Shekaru 18!

Amma shin ka taba jin Annabi Ayyub ya je wajen boka? Ya je wajen tsafi? Ya yanke kauna? Ya ce Allah bai ji ba?

A'a!

Abinda ya fada kawai shi ne addu'ar da har yanzu muke karantawa:

"Lallai ni, cuta ta shafe ni, kuma Kai ne Mafi rahamar masu rahma" [Anbiya:83]

Ba ya cewa "Ya Allah me yasa ni?" A'a, yana cewa "Ya Allah Kai ne mai rahma".

ME YA FARU A KARSHE?

Allah Ya ji addu'arsa. Allah Ya ce masa "Ka buga kasa da kafarka". Ya buga, ruwan zafi ya fito ya yi wanka, ya warke. Allah Ya mayar masa da dukiyarsa sau biyu, Ya mayar masa da 'ya'yansa.

Me yasa?

Saboda ya yi hakuri. Saboda bai je wajen boka ba.

YA KAI MAI CIWO A YAU:

Na san ka gaji da shan magani.
Na san kudi sun kare.
Na san wani na cewa "je ka je wajen boka, je wajen malam tsibbu".

Amma ka ji:

MUTUWA DA IMANI TA FI RAYUWA DA SHIRKA.

Ka mutu da cutar nan, ka je Aljanna, ya fi ka warke ta wajen boka ka je wuta.

Annabi S.A.W ya ce: "Duk wanda ya je wajen boka ya gaskata shi, ya kafirta da abinda aka saukar wa Muhammadu".

Boka ba zai warkar da kai ba. Zai kara maka cuta ce kawai - cutar shirka. Cutar jiki wata rana za ta warke ko ka mutu ka huta. Amma cutar shirka, sai mutum ya je wuta har abada.

ABINDA ZAKA YI YANZU:

1. Ka yi alwala ka yi Sallah: Ko a kwance kake, ka yi Sallah da idanunka.
2. Ka yawaita wannan addu'ar ta Annabi Ayyub: "Ya Allah cuta ta same ni, Kai ne Mafi rahamar masu rahma" - Rabbi anni massaniyad durru wa anta arhamur rahimin.
3. Ka nemi magani na halal: Je asibiti, sha magani, yi addu'a. Wannan Sunnah ne.
4. Ka yi hakuri: Kowane zafi da kake ji, zunubanka na gogewa.
5. Kada ka je wajen boka ko kadan: Ko da ace zasu yanka maka kaza, ko su ba ka rubutu, ko su ba ka ruwa. Duk shirka ne.

Ka tuna, Annabi Ayyub shekaru 18 yayi a cuta. Kai naka watanni ne ko shekara daya. Allah zai warkar da kai.

Cuta daga Allah jarrabawa ce, warkewa ma daga Allah ne.

Kada ka canja Ubangijin da zai warkar da kai don wani boka dan karya.

Zaka iya share ko turawa yan uwa marasa lafiya don samun ladan ka kaima

Allah Ya ba ka lafiya. Allah Ya goge maka zunubanka da wannan ciwon. Ka yi hakuri, Aljanna tana gaba.

🤲

22/09/2026

TO WAI TAYA ZAKAYI NASARA BAKA DA AIKI SAI KALLON BATSA?🤔

Idan kace rubutun yayi tsayi ai befi Rayuwar ka tsayi ba🙌

Wallahi kana rufe wa kanka kofar arziki da kanka.

Ilimin kimiyya (Neuroscience) ya tabbatar:

Kwakwalwar mutum tana aiki kamar Memory Card. Duk abin da ka gani da idonka, kwakwalwa tana haddace shi, tana ajiye shi.

Idan ka cika ta da batsa, da tsaraici, da mata tsirara, to waccan hoton baya gogewa. Zai zauna a kwakwalwarka.

Sai ya zama:
- Kana Sallah, hoton batsa ne a ranka.
- Kana karatu, hoton batsa ne a ranka.
- Kana zaune da mutane, kana tunanin batsa ne.
- Kana bacci, mafarkin batsa kake yi.

Kwakwalwa ta gurbace!

Taya wannan kwakwalwar da ta cika da haram zata yi tunanin kasuwanci? Zata yi tunanin kirkire-kirkire? Zata yi tunanin hanyar samun kudi na halal?

A'a, bazata iya ba.

Allah Ya ce: "Lalle zuciya idan ta baci, gaba daya jiki ya baci"

Ka cika zuciyarka da haram, sannan kake mamakin me yasa baka da natsuwa, me yasa baka da basira, me yasa baka da arzikin da kake so?

GASKIYAR KIMIYYA:

Masana sun gano:

1. Kallon batsa yana kashe sinadarin Dopamine a kwakwalwa. Wannan sinadarin shi ne yake baka kwarin gwiwar yin aiki, neman buri. Idan ya mutu, zaka zama laulayi, mara himma, baka son aiki, baka son karatu. Sai bacci da kwanciya.

2. Kallon batsa yana rage Focus. Bazaka iya mayar da hankali akan abu daya na minti 10 ba. Kullum hankalinka yana tashi. Taya zaka yi kasuwanci ko karatu da wannan kwakwalwar?

3. Kallon batsa yana sa ka kasa jin dadin halal. Matarka bazata maka dadi ba, saboda kwakwalwarka ta saba da abin da ya fi ta.

KA DUBA KANKA:

Yaro dan shekara 20-25, babu aiki, babu sana'a, babu karatu mai ma'ana, amma yana da waya mai data, dare har gari yana kallon batsa.

Safe ya tashi 11am, ido ya kumbura, kai ya yi nauyi, rana ta baci, ba wanka, ba addu'a, ba burin zuwa ko ina.

Wannan mutum taya zai yi nasara? Taya Allah zai bude masa kofar arziki alhali ya rufe kwakwalwarsa da najasa?

KANKA KA RUFE KANKA.

Arziki yana son kwakwalwa mai tsabta, mai tunani mai kyau, mai natsuwa.

Batsa tana kashe kwakwalwa, tana kashe natsuwa, tana kashe himma.

DAGA YAU:

Ka wanke kwakwalwarka kamar yadda kake wanke tufafinka.

Ka daina cika ta da haram.

Idan ka bar batsa na kwana 30 kawai, zaka ga:

- Hankalinka zai dawo
- Baccinka zai yi dadi
- Himmarka zata dawo
- Zaka fara tunanin abubuwan da zasu amfanar da kai

Allah baya azurta kwakwalwar da ta cika da haram da basira mai amfani.

Ka tsarkake kwakwalwarka, Allah zai tsarkake arzinkinka.

Zaka iya share don amfanar da yan Uwa
Se Mun sake haduwa🤝
Allah Ya tsare mu 🤲

21/09/2026

Sha'awa Fah😊 hmm
Gaskiya Duk Wanda Be karanta saqonnan ba ansha Dashi karka ce yayi tsayi Abune daze amfane ka duniya da lahira🥰

ALLAH YA HALICCI MALA'IKU DA HANKALI BA SHA'AWA, YA HALICCI DABBOBI DA SHA'AWA BA HANKALI, DAN ADAM YA HADA MASA BIYU

Wannan kalma ta malamai tana da zurfi sosai. Mu tsaya mu yi tunani.

1. MALA'IKU: Allah Ya halicce su da HANKALI kawai, ba su da SHA'AWA.
Saboda haka ba sa sabon Allah. Ba sa cin abinci, ba sa shan abin sha, ba sa aure, ba sa gajiya. Aikinsu kawai su ne bauta. Kamar na'ura mai aiki da hankali amma babu sha'awa.

2. DABBOBI: Allah Ya halicce su da SHA'AWA kawai, ba su da HANKALI.
Suna ci, suna sha, suna bacci, suna jima'i. Ba su san halal da haram ba. Ba su san wata Lahira ba. Duk inda sha'awarsu ta ja su, nan za su bi. Ba su da hankalin da zai hana su.

3. DAN ADAM: Allah Ya hada masa HANKALI da SHA'AWA a jiki daya.
Wannan shine jarrabawar da ta bambanta mu.

Allah Ya baka sha'awa ka so mace, ka so kudi, ka so abinci, ka so suna, ka so bacci.

Amma kuma Ya baka HANKALI - littafin da zai gaya maka: Wannan halal ne, wannan haram ne. Wannan lokacinsa ne, wannan ba lokacinsa ba ne. Wannan zai amfani Lahirarka, wannan zai cutar da ita.

YAKI YANA NAN A ZUCIYARKA:

Kullum akwai yaki tsakanin hankali da sha'awa.

- Sha'awa tana cewa: "Ka yi zina, babu wanda ya gani"
Hankali yana cewa: "Allah na ganinka, kuma akwai Lahira"

- Sha'awa tana cewa: "Ka ci riba, zaka samu kudi da sauri"
Hankali yana cewa: "Riba haram ce, albarkar kudin zata tafi"

- Sha'awa tana cewa: "Ka yi karya ka kubuta"
Hankali yana cewa: "Karya tana kai mutum Wuta"

IDAN KA BARI SHA'AWA TA RINJAYE HANKALI, TO KA ZAMA KAMAR DABBA.

Allah Ya ce:
"Shin ka ga wanda ya riki son zuciyarsa a matsayin abin bautarsa? ... Kamar dabbobi suke, a'a sun fi bacewa." [Furqan: 43-44]

Dabba tana bin sha'awarta ne saboda bata da hankali. Kai kuma kana da hankali amma ka ki amfani da shi, ka bi sha'awarka kawai. To ka fi dabba muni, domin ita uzuri take da shi, kai baka da shi.

Amma...

IDAN KA BARI HANKALI YA RINJAYE SHA'AWA, TO KA FI MALA'IKU DARAJA.

Mala'iku ba sa sabo saboda ba su da sha'awa. Ba jarrabawa bane gare su.

Kai kana da sha'awa mai karfi, amma ka danne ta, ka ce: "A'a, zan ji tsoron Allah."

Wannan dannewar - wannan shine abin da Mala'iku suke mamaki da shi. Wannan shine dalilin da yasa Allah Ya ce Mala'iku su yi sujada ga Adamu.

DARASI MAI GIRMA:

Yau tambayi kanka:

Waye yake mulkin rayuwarka? Hankalinka ko sha'awarka?

Idan wayarka ce, da kallon batsa, da son kudi ta kowace hanya, da bin matan banza - to ka koma dabbobi.

Amma idan ka tashi da asuba, ka ki bacci, ka je masallaci, ka rufe idonka daga haram, ka hanu ka daga haram, duk da sha'awarka tana so - to ka zama fiye da Mala'iku,

Mu dage mu bari hankali ya jagoranci sha'awa, ba sha'awa ta jagoranci hankali ba.

Kuyi share ku samu ladaa ko wanne dan adam yana buqatar wannan saqon
Se mun sake haduwa

Allah Ya datar da mu 🤲

18/04/2026

CIN ZARAFIN ADDINI DA TAUYE HAKKI NA DOKAR QASA!

Yanzu naga Labarin
Wata Daliba Musulma tazo zata shiga gurin da zasu rubuta jarabawa ta JAMB sai wata jami'ar tsaro na Civil Defence ta hanata shiga, ta koreta saboda hijabin ta

Amma ga wasu Dalibai sun zo tsirara an barsu sun shiga ba tare da wata tsangwama ba😢

Wannan cin zarafi da tauye hakkin addini da wulakanci ya faru ne a makarantar Peter Harvard School dake Kubwa a garin Abuja

Dokar Kasar Nigeria ya bawa kowa damar yin addininsa yadda ya ga dama ba tare da cutarwa, saka hijabi a gurin mace Musulma addini ne ba wai ganin dama ba

Abinda wannan jami'ar tsaro tayi fito na fito da dokar Kasa ne, wanda ya kamata a gudanar da kwakkwaran bincike domin ta fuskanci hukunci, domin zai iya haddasa fitina da tashin h@nkali

Kuma wannan yana kara bayyana mana cewa Musulmin Nigeria an gama cinye mu da yaki, ku yi tunanin in ba Musulma bace tazo zata shiga sai akace dole sai ta saka Hijabi? me kuke tunanin zai faru?

Yawan mu ya zama kamar bai da wani amfani, irin wannan wulakanci da cin fuska ya kamata ace ya jima da zama tsohon yayi🗣

Allah Yasa Mudace 🙌

Address

Dairah

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Smartdata4u posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Smartdata4u:

Share