Kiran Sayyed Zakzaky

Kiran Sayyed Zakzaky ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA,ALIY MUHAMMAD

Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Ya kawo cewa:“Allah Ta'ala yana cewa:يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تَنْصُرُوا ا...
19/05/2026

Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Ya kawo cewa:

“Allah Ta'ala yana cewa:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ يَنْصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ.

“Ya ku Muminai, idan kuka taimaki addinin Allah, Allah zai taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduginku.”

“Wannan alƙawari ne na Allah. Saboda haka, mu a nan har yanzu (azzalumai) suna tunanin kawai za su muttsike mu ne. Saboda haka, muna marhalan dauriya ne. Amma sun san cewa, marhala-marhala ne, akwai marhalan da yana nan tafe!

“La-muhalata yana tafe. Wannan ne lokacin da kuma tursasa mana din ba fa zai yiwu ba, mun fi ƙarfin wannan kuma.

“Hawa-hawa ne. Su ma s**an fada, s**an ce ya k**ata su gama da abin ne (Da'awa) tun bai yi karfi ba. Su ba su suna kuka suna yin ne yana ƙara ƙarfi ba. Da ma za su kyale ma, da sai ya daina ƙarfin. Amma ba za su ƙyale ba fa....

“Saboda haka, ina gaya mana ne, dole ne marhalan dauriya na nan, in babu wannan jarabawa, to tamkar ba Tabligin ake yi ba, domin Sunnar hanyar kenan. Ba canji ga wannan Sunnar kuma. Ita kenan, haka al'amarin ya gada. Haka aka yi ma na farko, haka za a yi ma na karshe, amma dai alƙawarin nasara Alhamdulillahi, Allah Ta'ala Ya yi mana.”

— A jawabinsa ga Muballigun, a yayin rufe Mu'utamar ɗin Lijanut Tarbiya wat-Tableeg, a ranar 15 ga Zulƙa'ada 1447 (3/5/2026) a gidansa da ke Abuja.

RANA TA FARKO: An Fara Gabatar Da Gagarumin Mu'utamar Ɗin Ƙasa Da Ƙasa A Jihar BauchiA yau Alhamis 16/04/2026 wanda ya y...
16/04/2026

RANA TA FARKO: An Fara Gabatar Da Gagarumin Mu'utamar Ɗin Ƙasa Da Ƙasa A Jihar Bauchi

A yau Alhamis 16/04/2026 wanda ya yi daidai da (28-10-1447H) ƴan’uwa musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky [H], sun fara gabatar da taron Mu'utamar ɗin ƙasa da ƙasa a jihar Bauchi, wanda taron shi ne karo na biyar da Harkar musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky [H] ke gabatarwa tun bayan waƙi'ar Buhari, domin kwakkwafa tunanin ƴan’uwa ƴan gwagwarmaya akan Fikira ingantacciya.

Shaikh Rabi'u Funtua, shi ne ya albarkaci taron da buɗewa da addu'a, sai mawaƙa su haskaka muhallin da waƙoƙi na shajja'a al'umma kan taimakon raunana da yaƙi da zalunci, da tsayawa ƙyam a kan tafarkin gaskiya.

Daga nan Sista Zahra'u Abubakar Katsina, ta karanto wasu ayoyi daga Alkur'ani mai girma cikin suratul Hujrat. Ɗan uwa Sidi Jawad ne ya gabatar da jawabin barka da zuwa.

Malama Maryam Sani ta gabatar da jawabin maƙasudin taro wanda ta bayyana cewa: "Idan kaje makaranta ka san cewa akwai abubuwan da za ka amfana da su, saboda haka akwai biro da takardar ka, da ka ji wani abu da baka sani ba, za ka rubuta. Wannan abin da ka tsinta, za ka yi amfani da shi, kuma sannan ka amfanar da wasu. Mun san cewa da yawan mutane suna son zuwa amma ba su samu zuwa ba. Wasu akwai dalilin rashin lafiya, wasu wani abu daban, wasu rashin kuɗin mota", in ji ta.

Ta ƙara da cewa: "Yana da kyau duk abin da muka ji, mu kai ma ƴan’uwan waɗanda ba su samu damar halarta ba, za mu samu ladan ji, zamu samu ladan isar da saƙo zuwa ga ƴan’uwan mu. Sannan yana da kyau duk abin da za mu yi a nan, ya kasance koyarwa ce ta addini, k**ar yadda muka sani mu masu da'awa ne, masu isar da saƙo ne. Duk abin da za mu yi, halayar mu wanda zamu nuna a nan, ya zama addini ne. Mu yi mu'amala k**ar yadda Allah ya ce mu yi."

Ta ƙara da jan hankalin Sistoci a kan kula da hijabi. Inda ta ce; "Mu kula da hijabanmu, mu yi ƙoƙari mu kiyaye shi", ta jaddada.

Bayan kammala jawabinta, wakilin ƴan uwa na Bauchi Shaikh Ahmad Yusuf Yashi, ya gabatar da jawabin maraba da baƙi. Daga ƙarshe aka yi addu'a aka sallami kowa zuwa masauki.

—Dandalin Yaɗa Labarai Na Taron


Rikicin Siyasar Samun Yanci Kai A Kano 1953 Wanda Akafi Sani Da Turanci (Kano Riot)Abin da ya jawo wannan tarzoma shi ne...
05/04/2026

Rikicin Siyasar Samun Yanci Kai A Kano 1953 Wanda Akafi Sani Da Turanci (Kano Riot)

Abin da ya jawo wannan tarzoma shi ne tabarbarewar dangantakar da ke tsakanin shugabannin siyasar Arewa da na Kudu a kan batun cin gashin kai a shekarar 1956. Wannan ya taso ne tun a shekarar 1953 da aka gabatar wa Majalisar Wakilai ta 1953.

Memba na Jama'iyar Action Group (AG), Cif Anthony Enahoro ya gabatar da kudiri a shekarar 1953 cewa: lokaci yayi da Najeriya zata samu ‘yancin kai a shekarar 1956. Shugabannin Arewa sun yi watsi da wannan kudiri. Lamarin ya ci tura wanda hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanin shugabannin siyasar Arewa da na Kudu.

Kayar da kudirin ya harzuka jama’ar Legas, inda s**a mayar da martani Mai Zafi ga shugabannin siyasar Arewa inda s**a yi ta yi musu ihu da zagi a Legas, bayan dage zaman Majalisar a ranar 31 ga Maris, 1953.

Jam’iyyar (AG PARTY) ta ’yan kabilar Yarabawa ce zalla, (NCNC) ita kuma ta kabilar Igbo ce, kuma dukkansu sun amince da ’yancin kai a 1956, alhali kuwa ita Jam'iyar (NPC), wanda itace Jam'iyar Arewa tace bata amince ba. Sardauna jagoran Jam'iyar Yace: Arewa ba ta shirya a ba da mulki ba, dalilinsa shi ne, yan Arewa da yawa basu kammala karatun jami'a ba, su kuwa yan kudu tuni sunyi nisa a karatun boko, ba k**ar yan Arewa ba. Sardauna da sauran mayan Arewa sunji tsoron idan an bayar da mulki a 1956 yan kudu za su mamaye dukkan manyan muk**ai a Najeriya.

Wannan yasa Yan kudu su kai ta zagin Sardauna suna cewa ya hada baki da turawan mulkin mallaka don ka da a bai wa Najeriya yanci.

Da lokaci ya kure, AG da NCNC sun tura wasu mutane kano domin yin kamfen din goyon bayan neman yanci, hakan ya haifar da tashin hankali a Arewa lokacin da kungiyar Action Group ta ziyarci Kano a karshen mako na 15-17 ga Mayu, lamarin ya faru ne sak**akon kiyayyar da aka nunawa yan Arewa a Legas.

Da farko dai an gudanar da zanga-zangar cikin lumana wanda magoya bayan jam’iyyar Peoples Congress ta Arewa s**a gudanar

Amma washegari zanga-zangar ta rikide ta koma tarzoma.

Tashin hankalin ya fara ne a Otal din Turawan mulkin mallaka, a ranar 16 ga Mayu 1953 wanda a wurin za ayi taron jam'iyar Action Group karkashin jagorancin Akintola.

Kafin taron dai kungiyar ‘yan asalin Kano ta janye goyan bayanta da izinin da ta bayar nayin wannan taro. Daga bisani wasu gungun jama’a ne s**a taru a wajen otal din, inda s**a fara jifan mutanen da ke kusa da otal din, yayin da s**a tafka asara mai dinbin Yawa. Wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ’yan Kudu ne sun mutu, daga bisani ’yan tarzomar sun yi yunkurin shiga Sabon Gari, amma jami’an ‘yan sandan kasar s**a fatattake su.

Lamarin ya kara ta’azzara kuma ya zama rikicin kabilanci a ranar 17 ga watan Mayu, lokacin da zauna Gari banza s**a fito daga yankin Arewacin Kano, musamman unguwar Fagge, wasu daga cikin masu tayar da tarzoma na dauke da bindigogi, s**a yi yunkurin kutsawa yankin Kudu da Ibo s**a mamaye yankin Sabon Gari, su kai sa'ar shiga, duk da cewa lamarin nasu na asali na kin Yarabawa ne, amma wadanda aka kashe a yankin Sabon Gari yawancinsu 'yan kabilar Igbo ne. Shaguna da suke ciki duk an wawashe su a Kasuwar Sabon Gari tare da kai munanan hare-hare.

An kira jami’an ‘yan sanda da na Sojoji tare da hana wasu barayin shiga yankin Sabon Garin. Rikicin ya ci gaba da barkewa a yankunan Kano musamman ma Fagge.

Bayan dokar hana fita a ranar 16 ga Mayu fadan ya lafa amma ya sake barkewa a washegari. A ranar 18 ga wata, an kai wani gagarumin dauki na 'yan sanda da sojoji zuwa Kano, an kuma kafa dokar ta-baci a duk fadin yankin. kuma an raba bangarorin da ke gaba da juna ta hanyar sa shingen waya.

Bayan Kura ta Lafa, an yi musayar fursunoni don a rage zaman dar-dar, an sako ’yan Kudu da aka k**a, su ma ’yan Arewa sun saki yan kudu, an bukaci ‘yan Arewa mazauna yankin Sabon Gari da su tashi, sannan aka bukaci ‘yan Kudu mazauna yankin Fagge da su koma Sabon Gari.

Kimanin ‘yan Najeriya 46 galibi ‘yan Arewa da kuma ‘yan kabilar Igbo ne s**a mutu a wannan arangamar, kuma an yi jinyar fiye da mutane 200 da s**a samu raunuka. Duk da cewa nan take gwamnatin mulkin mallaka a Najeriya ta kira abinda ya faru da rikicin kabilanci, amma shugabannin siyasa sun ce rikicin siyasa ne tsakanin mutanen da ke son mulkin kai a shekarar 1956 da kuma masu son ci gaba da mulkin mallaka.

Address

Zaria

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00

Telephone

08039297422

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kiran Sayyed Zakzaky posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share