09/03/2026
DA ƊUMI-ƊUMINSA: Gwamna Fintiri Ya Saka Dokar Hana Fita Na Sa'o'i 24 A Lamurde
Sakamakon sake ɓarkewar rikici da tashe-tashen hankula, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Ƙaramar Hukumar Lamurde, wadda za ta fara aiki nan take.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar a yau, an bayar da kakkausan umarni ga jami'an tsaro da su tabbatar da bin wannan doka sau-da-ƙafa, tare da damƙe duk wanda aka samu ya saɓa mata. Gwamnatin ta roƙi mazauna yankin da su bi doka, sannan su ba jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar tona asirin ɓata gari domin dawo da zaman lafiya.