17/09/2026
Daliban Arewa sun goyi bayan Tinubu a zaben 2027
Shugabannin dalibai daga manyan makarantu da ke jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.
Daliban, waɗanda s**a fito daga jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma kwalejojin ilimi, sun bayyana matsayinsu ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da ɓangaren dalibai na ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A).
Mai kula da ɓangaren daliban na A4A, Abdulmudallib Sheriff, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Dalibai (SUG) ta Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce goyon bayan nasu ya samo asali ne daga matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka a fannin ilimi, tallafin ɗalibai, koyar da sana’o’i da kuma bunƙasa matasa.
Sheriff ya ce ƙungiyar za ta fara gudanar da gangamin wayar da kan dalibai da neman goyon baya ga shugaban ƙasar a jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi.
Ya ce: “Muna tare da Asiwaju. Goyon bayanmu ba na baki kawai ba ne; tsari ne, an shirya shi kuma a shirye muke mu aiwatar da shi. Za mu kai wannan saƙo zuwa makarantu da al’ummominmu, mu wayar da kai, mu shirya tare da tattara mutane.”
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya danganta goyon bayan daliban da abin da ya kira manyan nasarorin gwamnatin Tinubu a fannonin ilimi, ababen more rayuwa, kiwon lafiya da noma.
Gwamnan ya ce matakan gwamnati na mayar da hankali kan ilimi da koyar da sana’o’in fasaha sun fi muhimmanci ga yankin Arewa, musamman shirin Technical and Vocational Education and Training (TVET) da Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND).
A cewarsa, bai kamata a tsaya kan tallafawa matasa ta fuskar ilimi kawai ba, sai an samar musu da damar tattalin arziki da fasahar zamani.
Uba Sani ya ce bayanan shirye-shiryen sun nuna cewa Arewa na da sama da kashi 60 cikin 100 na masu cin gajiyar wasu muhimman tsare-tsaren gwamnati.