21/04/2026
GreatestHighlights
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN. 😭
A yau Talata 21/04/2026, da misalin ƙarfe 3:27 na rana.
An samu wani mummunan lamari a Tsangayar Alkamatu da ke Gombe, inda masu taron siyasa na jam’iyyar APC s**a fesa wani sinadari mai tsananin cutarwa.
Wannan lamari ya shafi yara ƙanana sama da dubu ɗaya a wannan makaranta, waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba. Har yanzu akwai yara da dama da ba su dawo cikin hayyacinsu ba, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin shawo kan matsalar.
Shi kan shi Gwani Alkamatu Hussaini a halin yanzu ya kamu da rashin lafiya sakamakon wannan abu.
Saboda haka, muna roƙon Allah da Ya saka mana, kuma duk wanda ya jawo wannan cutarwa, Allah Ya hukunta shi da adalci.
‘Yan'uwa muna roƙon ku da ku taya mu da addu’a, Allah Ya bi mana haƙƙinmu.
Ku taimaka ku yaɗa wannan saƙo domin a san abin da ya faru.
Abin takaici ne yadda har kafin a kai ga wani mataki, wasu ‘yan siyasa s**a fara cutar da mu, alhali a tsawon lokacin mulkinsu ba su amfanar da mu da komai ba.
Allah Ka tarwatsa duk wani zalunci, Ka kuma kare al’umma daga irin wannan fitina.
Zan ɗora bidiyo domin a ga yadda abin ya faru, da irin halin da yara s**a shiga sakamakon wannan sinadari.
Daga Gwani Alkamatu.
Yasir Gwani Badamasi Pro