14/12/2025
😍🥺💔
Babban abin da ke jawo kuskuren fahimta tsakanin mutane shi ne: tunaninmu cewa duk abin da muke gani a zahiri, to shi ne gaskiya…
Da kuma cewa fuskokin mutane madubin zuciyarsu ne. Har wani karin magana "Labarin zuciya a tambayi fuska"
Alhali kuwa gaskiya ita ce: mutum halitta ce mai ban mamaki…
Yakan yi murmushi don ɓoye karyewarsa, yakan yi dariya don rufe raɗaɗinsa, ya kan bayyana ƙarfi da jarumta, alhali yana dab da faɗuwa.
Mutane ba sa rayuwa ba tare da raunuka ba; Kowane mutum yana da wani yaƙi da yake gwabzawa a zuciyarsa, wanda babu wanda ya sani:
Akwai abin da yake tsoro wanda bai furta ba, akwai tunanin da ke ƙona masa rai, akwai tambayar da ke hana shi barci.
Saboda haka, bai kamata mu yi hukunci kan mutum bisa shirunsa ba, ko murmushin fuskarsa kawai ba, ko idan ya bayyana tsanani ko nisa da mutane ba…
Musamman Idan mutum ya bayyana wani abu, wanda an san ba halinsa ba ne.
Wanda ya yi shiru, wataƙila yana fama da abin da ya kasa faɗi…
Wanda yake ware kansa da nisanta kansa, wataƙila shi ne mafi buƙatar ƙauna…
Ba duk wanda ya yi shiru ne yake cikin natsuwa ba…
Ba kuma duk wanda ya yi murmushi ne yake cikin farin ciki ba…
Akwai zuƙatan da ke neman taimako, ba tare da sun fitar da murya ba.
Allah ba Ya auna mu da ƙarfimu…
Allah Ya shiga lamarinmu, Ya ƙarfafi zuƙatanmu, Ya yaye mana dukkan damuwa.
Amin🤲🤲🤲