06/08/2026
JAMI'AR NORTHWEST UNIVERSITY, KANO TA SAKI CUT OFF MARKS NA KAKAR KARATU TA 2026/2027 WEDNESDAY 5TH, AUGUST 2026.
Jami'ar Northwest University, Kano Na Sanar Da Dukkan Daliban Daliban Da S**ayi Jamb 2026 Da Wanda S**a Cike D.E 2026 S**a Sanya Ta A First Choice Dinsu Cewar Ta Fara Siyar Musu Form Din Register Post Utme Da Direct Entry Daga Litinin 10th, August 2026 Zuwa Sunday 23rd, August 2026.
Wanda Suke Nema Ta Hanyar Jamb Su Tabbata Sun Sanya Jami'ar Northwest A First Choice Dinsu, Idan Ba Ita Bace A First Choice Dinku Kuje Kuyi Green Card Ku Sanya Ta, Wanda Zasuyi Green Card Din Su Tabbata Sunyi Nan Da 9th, August 2026.
Idan Course Din Da Ka Nema A Makarantar A Jikin Cut Off Marks Dinka Makinka Bai Kai Ba, Kaima Sai Kaje Kayi Green Card A Cbt Center Mafi Kusa Dakai Sai Ka Sanya Course Din Da Makinka Yakai, Idan Kasa Course Din Da Makinka Bai Kai Ba Ko Da Maki Daya Ne Kasani Bazaiyiwu Kayi Registration Na Post Utme A Haka Ba, Dole Saidai Ka Sanya Course Din Da Makinka Na Jamb Yakai Ko Ya Haura Haka Ake Bukata.
Wanda S**a Sanya Jami'ar Northwest Din A First Choice Zasu Iya Yin Registration Na Post Utme Dinsu Ayanzu, Daliban D.E Suma Haka.
Daliban D.E Wanda S**ayi DIPLOMA, Wajibi Ne Wanda S**ayi Bangaren Sciences Ya Kasance CGPA Dinsu Yakai 3.00 Sannan 3.5 Ga Wanda Suke A Bangaren Arts, Wanda Suke Nema Da NCE Wajibi Ne Point Dinku Yakai 9 Zuwa Sama, Sannan Masu IJMB Kuma 8 Points. Daliban D.E Zaku Iya Fara Siyan D.E FORM Dinku Ta Hanyar Online.
Wanda S**a Yi Jamb Kuma Zaku Iya Fara Registration Na Post Utme, Amma Duk Wanda Makinsa Ko Daya Ne Bai Kai Ba A Course Din Da Yake Nema Wajibi Ne Sai Yayi Green Card Yasa Wanda Makinsa Yakai.