07/12/2025
đź§… Noman Albasa a Lokacin Rani: Abubuwa 6 Da Manomi Ya Kamata Ya Kula Da Su
Noman albasa a lokacin rani yana buƙatar kulawa ta musamman da dabaru na zamani. Ga manyan abubuwa guda 6 da ya dace kowane manomi ya kula da su domin samun albarka da riba:
1. Sanin yadda ake yafen irin albasa:
Manomi ya kamata ya san lokacin da ya fi dacewa da yafen iri da kuma hanyar da tafi inganci wajen yin sa.
2. Fahimtar matakan noman albasa:
Ana noman albasa a matakai uku:
– Noman lawashi kawai
– Noman lawashi da ƙwayar albasa
– Noman ƙwayar albasa kawai, ba tare da lawashi ba
3. Zabin irin da ya dace:
Samun iri mai inganci yana da matuƙar muhimmanci domin ya haifar da amfanin gona mai yawa da kuma ingantacce.
4. Kulawa da tsarin ban ruwa:
Rani na buƙatar tsayayyen tsarin ban ruwa domin gujewa bushewar shuka da rage yawan hasarar amfanin gona.
5. Ingancin ƙasa da amfani da taki:
Albasa tana buƙatar ƙasa mai ɗan danko, mai riƙe danshi, ba mai yashi sosai ba. Haka kuma, amfani da takin gargajiya kamar *kashin kaji da toka* na ƙara wa shuka ƙarfi da inganci.
6. Lura da cututtuka da kwari:
Yin amfani da magungunan zamani don hana kwari da cututtuka masu kamawa lawashi ko ƙwayar albasa yana taimakawa wajen samun riba mai yawa kafin girbi.