13/07/2026
Dan tsakiyar da ya fi ‘yan gaba hatsari a tawagar Ingila: Bellingham ya kafa sabon tarihi...
A gasar da ake tsammanin ‘yan gaba ne za su mamaye kanun labarai, sai ga Jude Bellingham ya juya labarin gaba ɗaya—ba tare da kasancewa striker ba.
Tauraron England ya kafa wani tarihi mai nauyi, inda ya zama ɗan wasan Ingila da ya fi kowa zura kwallaye a bude (open play) a World Cup guda ɗaya. Wannan ba ƙaramin abu ba ne, domin ya zarce sunaye da aka saba jingina wa wannan matsayi—musamman ‘yan gaba da aka gina domin zura kwallo.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda yake yin wannan aikin cikin sauƙi, kamar ba sabon abu ba ne. Yana fitowa daga tsakiyar fili, yana shiga cikin sarari, sannan ya zama wanda ke kammala harin—abin da yawanci ake barin ‘yan gaba su yi.
Wannan ya nuna cewa Bellingham ba kawai ɗan wasa ba ne mai baiwa, illa wani sabon salo ne a kwallon kafa. Dan tsakiyar da zai iya jagoranci wasa, ya kare, sannan kuma ya zama mai kawo ƙarshe a gaba. Wannan ne ya sa yake zama barazana a kowane lokaci.
A cikin wannan gasar, ya nuna cewa matsayi ba ya hana tasiri. Ba sai ka zama striker ba kafin ka zama tauraron da ke yanke hukunci a wasa. Wannan ne ya bambanta shi da sauran.
Aminchi Sports na ganin cewa wannan tarihi da ya kafa ba wai kawai rikodi ba ne, alama ce cewa sabon zamani na ‘yan wasa ya zo—inda iyaka tsakanin matsayi ke rushewa.
Yanzu tambaya ita ce, shin Bellingham zai iya ci gaba da wannan abin mamaki har ya kai England ga daukar kofin duniya?
Ku fa, a ganinku ya kamata a ci gaba da kiransa dan tsakiyar fili, ko lokaci ya yi da za a fara kallonsa a matsayin cikakken mai zura kwallo?