09/04/2023
Farkon abunda zamu fara koya shine yadda zamuyi amfani da “Terminal” a Linux dinmu ko kuma Termux dinmu.
Dan haka yanzu ga wasu cammands masu sauki da muke bukatar saninsu.
1) pwd – “print working directory”
shi wannan command din ana amfani dashine domin sanin a wanne directory mutum yake aiki, idan ance directory a command line ana nufin “folder” idan mutum yana amfani da “GUI” ma’ana graphical user interface.
2) cd – “change directory”
shi kuma k**ar yadda sunansa ya nuna, yana nufin ka canja daga folder din dake zuwa wata folder din.
3) ls – “List contents in the directory”
Shikuma yana nuna mana dukkanin abubuwan da suke cikin directory din mutum k**a daga kan folders, files da dai sauransu.
4) mkdir – “Make directory”
Da wannan command dinne mutum zai kirkiri folder, sannan ya ajiye abubuwanda yakesan ajiyewa,
5) cp – “Copy”
zaka iya copy na file daga wani directory din zuwa wani da wannan command din na cp.
6) mv – “move or rename”
zaka iya tura file daga current folder dinka zuwa wata mai makon kayi copy nashi, sannan zaka iya amfani da wannan command na “mv” ka sauyawa wani file ko directory suna.
7) rm – “Remove”
Idan kanasan goge file wannan command din shi zakai amfani dashi, amma idan folder kakesan gogewa to dole sai kayi “forcing” nashi, sai command din ya kasance k**ar haka, (rm -rf ).
MISALAI:
1. Da farko zanfara da kirkirar folder wato directory, zan bashi suna NAMU
~$ mkdir NAMU
yanzu na kirkiri directory mai suna NAMU
2) zanyi amfani da cd domin in canza zuwa NAMU directory
~$ cd NAMU
3) tayaya zansan cewa yanzu na canza directory zuwa NAMU? Shine sai muyi amfani da command ls.
~$ ls NAMU
bayan mun danna enter zamuga yanxu muna cikin directory NAMU, kuma zai sauya kala zuwa “Blue” ya danganta da yadda mutum ya tsara terminal din tasa
~/NAMU $
Zakuma mu iya kara kirkirar wani directory din a cikin NAMU directory misali mubashi suna “jibril”
~/NAMU $ mkdir jibril
idan munaso mugane cewa mun kirkiri sabon directory sai muyi amfani da ls.
~/NAMU $ ls
jibril
~/NAMU $
yanzu bari mu canza zuwa sabon folder da muka bude mai suna jibril
~/NAMU $ cd jibril
~/NAMU/jibril $
To idan muka lura za muga cewa directory jibril yana cikin directory NAMU, dan haka daga nan zamu iya komawa duk directory din da mukesan komawa da taimakon cd(change directory)
Note: Muyi sani cewa command line suna da “case sensitive” ma’ana cd ba daidai yake da CD ba, hakana ls ba daidai yake da Ls ba, dan haka yadda aka gansu a karamin bakinsu to a haka mutum zaita amfanindasu.
Akwai screenshot na wasu commad din da mukai amfani dasu zan turasu, amma nayi sune a Termux masu amfani da wayar hannu kenan su zasufi ganewa duk da cewa haka command din yake hatta ga masu amfani da Linux din ko muka Mac.
Sannan littafin "command line" shima zan turashi ga masu bukata sai suyi download dinsa, domin zasu kara samun fahimta sosai.
~Namujibril