10/05/2025
ALKALI YA SANYA MATA SHARADIN YIN TSIRARA KAFIN KARBAR TAKARDAR SAKI DAGA MIJINTA.
Wata mata ta nemi saki daga wajen mijinta, sai alkalin kotu ya yanke hukunci da sharadin cewa dole ne sai ta cire duk tufafinta da yake jikinta ta zama tsirara kafin a ba ta takardar saki.
Amma sai abin da ba ayi zato ba ya faru! Eh, kada ku yi mamaki, wannan wani labari ne da ya faru a shekarun baya da s**a wuce a wani gari.
Akwai wani mutum da matarsa, inda s**a samu ɗan ƙaramin sabani a tsakaninsu.
Sai mahaifinta da ɗan uwanta s**a shiga lamarin, wanda hakan tasa lamarin ya tsananta har ta kai ga yan’uwanta su na neman saki daga wurin mijin.
Amma mijin ya ƙi amincewa da batun sakin, yana cewa sai dai abarsu su zauna su sasanta junansu, basu bukatar wani ya shigo cikin al'amarin, zasu iya shawo kan matsalolin da kansu.
Sabani ya ƙara kamari har sai da aka kai ga alkalin garin, bayan da al’ummar garin sun ji abin yayi yawa s**a shigar da korafi.
Alkalin ya tara su duka su huɗun: mijin, matar, mahaifi da ɗan uwan matar, ya ce:
"Tun da kun matsa akan lallai sai ya sake ta," yake shaidawa dangin matar, "to akwai wani sharaɗi da zan shimfida kafin a zartar da sakin!"
Wannan ya ba su mamaki matuƙa, domin ba kasafai alkalai ke sanya sharudda a hukuncin saki ba.
Sai s**a tambaye shi menene sharaɗin?
Alkalin ya juyo ga matar ya ce mata:
"Dole ne ki cire duka tufafinki idan har kina so ki samu sakinki."
Matar ta ƙi yarda da sharadin hakan, sai Alkali ya sassauta hukuncin ya ce:
"Ki zaɓi mutum guda ɗaya daga cikinsu wanda zaki iya Keɓantuwa dashi sannan ki cire tufafinki."
A nan ne abin mamaki ya faru—duk da cewa mahaifinta da ɗan uwanta suna nan a gurin, matar nan sai ta zaɓi mijinta.
Sai alkalin ya yi dariya, ya kalle ta ya ce:
"‘Yata, miji ne kaɗai ke iya rufe asirin matar sa ya tsare mutuncita ya bata kariya. Ku tafi gida tare da mijinki."
Sannan ya kalli kowa ya ce: "Maganar ta ƙare.
KU FITO MANA DA DARUSSAN DA KUKA DAUKA DAGA CIKIN WANNAN LABARIN.