01/06/2026
Rikicin cikin gida a jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ya ƙara tsananta bayan musayar kalamai da zarge-zarge tsakanin tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani, da Babban Mai Bai Wa Gwamna Uba Sani Shawara Kan Harkokin Siyasa, Muhammad Abubakar Mamadi.
Zailani ya zargi wasu shugabannin jam’iyyar da yin maguɗi a zaɓukan fidda gwani na APC tare da yaudarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan wasu batutuwan siyasa. Ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan abubuwa na iya raunana jam’iyyar kafin zaɓuɓɓuka masu zuwa.
Sai dai a martaninsa, Muhammad Abubakar Mamadi ya ƙaryata wasu daga cikin zarge-zargen, yana mai cewa shi da Zailani tare da wasu mutane sun taɓa rubuta sakamakon zaɓe a Ƙaramar Hukumar Igabi a baya.
Mamadi ya kuma yi wani zargi mai ɗaukar hankali inda ya ce akwai lokacin da shi da Zailani s**a gudu tare bayan da ‘yan sanda s**a fara nemansu. Wannan ikirari ya ƙara jawo hankalin jama’a kan rikicin da ke tsakanin ‘yan siyasar biyu.
Har ila yau, Mamadi ya yi iƙirarin cewa s**ar da Zailani ke yi wa wasu shugabannin APC na da alaƙa da rasa tasirin siyasa da yake da shi a cikin jam’iyyar.
Musayar zarge-zargen ta haifar da martani daban-daban daga jama’a tare da sake tayar da tambayoyi kan sahihancin wasu zaɓukan da aka gudanar a baya a jihar.
Rahotanni na nuni da cewa rikicin na ci gaba da ɗaukar sabon salo yayin da bangarorin ke ci gaba da bayyana matsayinsu a bainar jama’a.