29/07/2026
DEGREE KAƊAI BAI ISA BA: GASKIYAR DA YA KAMATA MATASA SU FAHIMTA A YAU A NIGERIA
A baya, samun degree ana kallonsa a matsayin babbar hanya zuwa samun aiki mai kyau da rayuwa mai sauƙi. Amma a yau, abubuwa sun canza. A Najeriya, samun takardar shaidar karatu kaɗai ba ya ba da tabbacin samun aiki, domin masu neman aiki sun yi yawa, yayin da guraben aiki ba su wadatar da kowa ba.
Babban kuskuren da wasu matasa suke yi shi ne su dogara da degree kawai, su manta cewa duniya ta koma zamanin ilimi tare da kwarewa (skills). Kamfanoni da masu ɗaukar ma'aikata suna neman mutum mai iya kawo mafita, ba wai mai takarda kawai ba.
Degree na da daraja, amma idan ba ka da wata kwarewa kamar fasahar zamani, sana'a, iya sadarwa, kirkira, amfani da fasaha ko wata kwarewa ta musamman, za ka iya samun kanka kana jiran aiki na dogon lokaci.
Kar ka bari shekaru na karatu su zama banza. Ka ƙara wa degree ɗinka daraja ta hanyar koyon abubuwan da kasuwa take bukata. Ka koyi sana'a, ka nemi kwarewa, ka gina kanka.
Ka tuna: Takarda na iya buɗe maka ƙofa, amma skills ne za su taimaka maka ka zauna a ciki.
Lokacin da wasu suke neman aiki da degree kawai, masu hangen nesa suna gina kansu da ilimi, kwarewa da hazaka.
Makomarka tana hannunka. Kada ka jira gwamnati ko kamfani su koya maka abin da ya kamata ka koya wa kanka.
🖌️