21/07/2025
*ZUMA ROCK*
Zuma Rock dutse ne mai cike da tarihi wanda ke kusa da Abuja, amma yana cikin garin Madalla ne a Jihar Niger, ba a cikin birnin Abuja ba.
Wanda kimanin Tsawon dutsen daga ƙasa ya mita 300m, Jimillar tsayin shi kuma takai mita 725m
Tarihin Sunan Dutsen ya samo asali ne a ƙarni na 15, mutanen Zuba (Koro/Jukun) su s**a fara gano dutsen kuma suke kiran shi “Zumwa”, wato wurin Taron Fara saboda yawan farin dake rayuwa a yankin.
Mutane na yankin k**ar Gwari (Gbagyi) sun ɗauki Zuma Rock a matsayin dutse mai wata gagarumar alfarma domin suna amfani da shi wajen ibada, da kuma tsare kai a lokacin yaƙe-yaƙe domin basu kariya.
Akwai wata siffar fuska a jikin dutsen da ke k**a da ido, hanci da kuma baki wanda ruwa ke zubowa ta wurin. Ana ɗaukar wannan fuska a matsayin ruhin kakanni ko kuma wata alama dake nuna akwai mutanen ɓoye (aljanu).
Hawan dutsen yana ɗaukar kimanin awanni biyar (5) kafin a isa saman shi, kuma daga saman ana iya ganin yawan filaye, da manyan gine-ginen da ke kewaye da Abuja.
Mutane na zuwa Zuma Rock don ɗaukar hoto, da shakatawa, da kuma masu sha'awan hawan dutse musamman a lokacin bazara, wato lokacin da ba ruwa, domin tituna suna bushe.
Wasu mutane na cewa dutsen yana iya fitar da wuta a lokacin ruwan sama, wanda ke sauyawa ta koma nau'in haske ko wutar lantarki.
Ana yawan jin labarai cewa Zuma Rock na da tsafi ko kuma yana da cin ruhin mutane, amma a wani ƙaulin kuma dutsen kariya ne ga yankin daga masifu.
Wasu kuma na cewa yana da bada mafaka ga masu tsafe-tsafe ko Aljannu musamman saboda wani sautin ban mamaki da ake ji na tashi daga dutsen lokaci bayan lokaci.
Tun daga shekarar 1999, an saka Zuma Rock a takardar kuɗin ₦100 ta Najeria a matsayin wata alama ta ƙasa.
Zuma Rock na ɗaya daga cikin manyan al’adun halitta da ke cike da tarihi da kuma al’ajabi a Najeriya🇳🇬.
👉Kuyi Following Shafin mu ✅ domin cigaba da Binchiko🔍 muku wurare da abubuwa masu ban Al'ajabi.com
📝AMD