20/09/2026
SANARWA GA MATASA
iDICE PROGRAMME – DAMAR KOYON FASAHA DA KIRKIRE-KIRKIRE
Investment in Digital and Creative Enterprises (iDICE) shiri ne na Gwamnatin Tarayya, wanda Bank of Industry (BOI) ke aiwatarwa, tare da haɗin gwiwar African Development Bank (AfDB), Agence Française de Développement (AFD), da Islamic Development Bank (IsDB).
Shirin yana ba matasa damar samun digital da creative skills, haɓaka ƙwarewar kasuwanci, da samun damar shiga ayyukan yi, internships da sauran damar ci gaba.
A wannan zamani, technology na daga cikin manyan hanyoyin samun ilimi, aiki da kasuwanci. Samun ƙwarewar zamani na iya taimaka wa matashi wajen yin aiki online, freelancing, ƙirƙirar sana’a ko kasuwanci, da kuma samun damar shiga sabbin guraben aiki.
KA YI RAJISTA:
Ana gayyatar matasa masu sha'awa su yi rajista ta hanyar official link ɗin:
https://www.activityinfo.org/c/ci0vzd6mseisjr9fo/e026f9
GABATARWAR SHIRIN A GUMEL
Za a gudanar da taron gabatarwa da wayar da kan matasa game da shirin a:
- Gumel Emirate Foundation
- Talata, 22 ga Satumba 2026
- 10:00 na safe
Duk wanda yake fuskantar matsala wajen cike registration ko yake buƙatar ƙarin bayani zai iya tuntubar mu akan wadannan lambobin waya:
07066717675
09039499611
07062822399
Ko kuma a ziyarci:
Sahel Information Systems and Consultancy Services Limited (SISCO)
ICT Department, Gumel Emirate Foundation