Hanan TV

Hanan TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hanan TV, Information Technology Company, Near Haruna House Opp Central Primary School Shop No 6, .

25/11/2021

Waka abakin mai ita tafi dadi, chiyaman na Gwani ward Alh Audu yace babu shi acikin wadanda ake rade radin sun ajiya muk**ansu na jam'iyar APC a yamaltu Deba a yau 25 nuwanba 2021

24/11/2021

Bayan kammala jawabin shugaban matasan jam'iyar PDP na kasa wato, Prince Muhammad Kadade Suleiman, ga irin yadda masu ruwa da tsaki na PDP suke nuna masa soyayya da jin dadin jawabansa.

Wai shin jamm'iyar APC mai mulki ma haka suke da sauran mutanen cikin jamm'iyar nasu?

24/11/2021

Saukar Gwamnan jahar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, kenan a filin sauka da tashi na jirgin sama na lawanti dake Akko, bayan kammala ziyararsa na gaisuwan rasuwa a jahar legas inda yaje ta'aziyar Sani Dangote kanin babban attajirin dan kasuwan nan wato Alh Aliko Dangote.

18/11/2021

Da dumi dumin ta Hon Baffa Dadun Hamza, ya bayyana fice warsa daga jam'iyar APC mai mulki a jahar Gombe, ya koma Jam'iyarsa ta PDP a yau 18, nuwanba, 2021.

17/11/2021

'Shugaban cushe-cushe', Shekarau ya yi wa Ganduje gugar-zana

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi wa gwamnan Kano mai ci, Abdullahi Ganduje gugar zana a wani taron siyasa da ya gudanar a gidansa na Kano a yau Talata.

Yayin da zai fara jawabi a gurin taron, Shekarau ya yi gugar zana ga Ganduje da cewa "shugaban cushe-cushe".

Idan an tuna, jaridar DAILY NIGERIAN ta wallafa fefen bidiyon Ganduje yana cusa dalolin Amurka a aljihu, wanda ake zargin cin hanci ne yake karba daga hannun wani dan kwangila.

Tun daga nan hakan ya zama abin shaguɓe da gugar zana ga gwamnan.

A yayin da zai fara jawabi a gurin taron ,Shekaru ya fara da cewa "Alhajiji [Na-goda] ya ce shi ne shugaban karɓe-karɓe. To amma ina jiran sa ya fada wa ‘yan Kano waye shugaban cushe-cushe?"

Shekarau ya na faɗar haka, sai magoya bayansa su ka ruɗe da ihu da shewa.

Daga nan ne Sanatan ya ci gaba da ƙorafi a kan abubuwan da su ke faruwa a jam'iyar da har su ka sanya ya ware na shi ɓangaren, in da ya ce ya yi hakan ne domin ya ƙwatar wa ƴan jam'iya da al'ummar Kano ƴancin su.

Bugu-da-ƙari, Shekarau ya ce tun da Ganduje ya yi gaiyar ƴan jam'iya, har da Shugaban ta na ƙasa, Adams Oshiomole, s**a yi masa magiya ya shiga APC, sannan a ka ci zaɓe, gwamnan bai sake yin wani abu da shi na jam'iya ba.

Ya ƙara da cewa ko zaɓen shugabannin jam'iya na mazaɓa, ƙanan hukumomi da na jiha, gwamnan ne yai don ransa ba tare da an tafi da mutanensa ba.

Ya nanata cewa shi fa ba zai bar APC ba har sai ya ceci al'ummar Kano da ga mulkin k**a karya da a ke yi a jam'iyar, inda ya ce "jam'iyar ta zama ta gwamna, matar gwamna da shugaban ta."

Source: Daily Nigerian

14/10/2021

Follow us and get latest news on Hanan TV.

Address

Near Haruna House Opp Central Primary School Shop No 6

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hanan TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share