27/01/2026
Abin da Jarumi Mahesh Babu Ya Faɗa Game da Alkur’ani
Yan Ta’adda Ba Musulmi Ba Ne"
Lokacin da aka tambayi jarumin game da dangantakar ta’addanci da addinin Musulunci, sai ya ba da amsa a takaice amma mai cike da ma'ana: "’Yan ta’adda ba Musulmi ba ne."
Jarumin ya ƙara da cewa:
"Ba za a iya kiran su Musulmi ba, domin kuwa Manzo kuma Annabi Muhammad (SAW) bai taba aikata kowane nau'i na zalunci ga wani ɗan adam ko wata halitta ba a tsawon rayuwarsa."
Haka kuma, ya bayyana cewa Littafi Mai Tsarki na Alkur’ani ba ya koyar da ta’addanci. Hasali ma, Alkur’ani bai tsaya ga yin tir da ta’addanci kawai ba, a’a, ya ma haramta zaluntar kowace irin halitta.
Wanan maganar tasa Ina son Mahesh babu
Ya Allah yasa Kada ka mutu kana kafiri Allah ya dawo da kai hanyar gaskiya Mahesh babu.
Salis Trend