11/07/2026
AlhamdulilLahi ni Muazu Umar Muhammad Chairman Team network Nigeria a jiya ranar Juma a ne na samu ganawa da mai Girma Hon. Abdulhalim Liman Danmaliki wato dan majalissar tarayya mai jiran gado da yardar Allah
inda muka samu ya bamu lokaci mai tsawo muna tattaunawa bayan mun masa bayanin irin gudun mawarda mukeso mu bayar shima ya nunamana irin shirye shiryen da yakeda shi akan matasa da mata sai naji gaba daya abinda yake damuna shi yake damunsa domin yayi tsari a rubuce yadda zai gina matasa da mata
wasu abubuwan za a gudanar tun kafin zabe wasu kuma bayan Allah ya tabbatar za a dora aci gaba dan haka AlhamdulilLahi wannan tattaunawa da mukayi dashi tasa mun gamsu da nagartarsa kuma mun tabbatar baxai watsa mana kasa a idoba da izinin Allah
Daga karshe muna fata Allah ya mana jagora baki daya