Abba Umar Khetry

Abba Umar Khetry Tech • Security • Internet

📞 Shin Ka Taɓa Lura Wasu Lokuta Haka Siddan Ana Cire Maka Kuɗi Babu Gaira Ba Saba?Haka kawai sai ka ji mutane suna ƙoraf...
16/05/2026

📞 Shin Ka Taɓa Lura Wasu Lokuta Haka Siddan Ana Cire Maka Kuɗi Babu Gaira Ba Saba?

Haka kawai sai ka ji mutane suna ƙorafi akan katinsu ba ya daɗewa, ko ana sace musu wani kaso da zaran sun loda, kana mamakin dalilin da yasa ake cire musu kuɗi a layi ba tare da sun yi kira ko sun sayi data ba 😳

DALILIN SHI NE:
Lokuta da dama mutane suna Subscriptions na wasu Services da ake tallata musu ba tare da sun sani ba.

Wannan Code ɗin *305 # zai taimaka maka wajen:

✅ Duba Services da aka kunna a layinka,

✅ Ganin Services masu cire maka kuɗi,

✅ Dakatar da su duka, ko cire duk wanda ba ka buƙata.

📌 Ka tuna: *305 # yana aiki a dikkan kamfanonin layika da ag-garemu a Nigeria.

⚠️ SHAWARA: Duk lokacin da ka yi arba da sabon Saƙo ka tsaya da kyau ka karanta, domin sau tari tallace-tallace ne, kuma wasu tsarukan su ke sa ana cire mana kuɗi a waya.


Ku yi following ɗin Abba Umar Khetry domin samun shawarwari da kuma haske akan Tech & Cyber Security.

Abba Umar Khetry ™

Shin Ka Taɓa Tunanin Wani Zai Iya Ganinka, Da Sauraron Duk Abinda Kake Tattaunawa A Wayarka 😂?Eh, tabbas akwai yiwuwar h...
15/05/2026

Shin Ka Taɓa Tunanin Wani Zai Iya Ganinka, Da Sauraron Duk Abinda Kake Tattaunawa A Wayarka 😂?

Eh, tabbas akwai yiwuwar hakan a wasu lokuta.

Meyasa kake shiga da waya banɗaki?
~ Saboda akwai Network 😂

Meyasa ka saki jiki har kuke tattaunawar sirri a waya ko kuma wayar na kusa da ku?
~ Saboda ka cire Handsfree 😂

Ke! Meyasa kika tura wa miji ko saurayinki saƙo ta Messenger?
~ Saboda ba Ɓaci😂

Ƙaddara ma ba ɓaci, ka sani wasu apps marasa aminci ko malware na iya neman izinin amfani da Camera ko Microphone a waya. Idan an ba su Permission ba tare da la'akari ba, akwai yiwuwar su yi amfani da su fiye da yadda ake zato.

Idan wani ya samu damar sarrafa wayarka, hakan na iya ba shi damar gani da sauraron duk wani sirri na ka!

Don haka, ya k**ata kowa ya kula da abubuwan nan:

™ Ba kowane App ake ba Permission na yin amfani da Camera ko Microphone ba.

™ Ka kula da yadda wayarka ke yin zafi ko saurin ƙarewar caji ba tare da amfani mai yawa ba.

™ Kuma ka kula da Indicator na Camera ko Microphone a saman Notifications na wayarka.

✓ Yadda Zaka Kare Kanka™:

✅ Ka riƙa duba Permissions na Apps akai-akai (duk wani App dake da Permission na yin amfani da Camera ko Microphone ka tabbatar yana da aminci).

✅ Kada ka sauke Apps daga wuraren da ba ka yarda da su ba.

✅ Ka riƙa Updating na wayarka da Apps lokaci bayan lokaci. Sannan ka goge duk Apps ɗin da ba ka amfani da su ko waɗanda ba ka yarda da su ba.

NOTE: Ba duk lokacin da waya ta yi zafi ko batiri ya ragu bane Hacking. Amma yana da kyau a kula da duk wani sauyin da ba a saba da shi ba.

Ku yi following ɗin Abba Umar Khetry ™ domin samun muhimman shawarwari da haske akan Tech & Cyber Security.

Abba Umar Khetry ™

14/05/2026

📌 Shawara: Kada ka saka muhimman bayanai a website da ya fara da http://. Ka tabbatar yana da 🔒https://: kafin ka yarda da shi.

Bambanci Tsakanin HTTP da HTTPS (🔒)Duk lokacin da ka shiga wani website, zaka ga link ɗinsa yana farawa da http:// ko ku...
14/05/2026

Bambanci Tsakanin HTTP da HTTPS (🔒)

Duk lokacin da ka shiga wani website, zaka ga link ɗinsa yana farawa da http:// ko kuma https://. Menene bambancin su?

¹™ HTTP na nufin:
HyperText Transfer Protocol (HTTP): Wannan tsohon tsarin sadarwa ne tsakanin browser da website. A tsarin bayanai suna tafiya ba tare da kariya ba, hakan na nufin cikin sauƙi Hacker zai iya ganin bayanan da ka tura ko ka karɓa. Password, Email, Messages, da sauran bayanai duk suna tafiya a bayyane. Don haka duk website ɗin da ya fara da: http:// ba shi da cikakken tsaro!

²™ HTTPS na nufin:
HyperText Transfer Protocol Secure (HTTPS): Asalinsa HTTP ne sai aka ƙara masa fasahar kariya ta SSL/TLS encryption. A wannan tsarin bayanai suna tafiya a ɓoye. Password, Bank details, Messages, da sauran Personal information duk suna cikin kariya.

NOTE: Idan ka ga alamar kwaɗo (🔒) a kusa da link ɗin kowane website musamman a browser, to hakan na nufin HTTPS ne.

Taƙaitaccen Bambanci Tsakaninsu Shi ne:

™ HTTP: yana farawa da http://
™ HTTPS: kuwa yana farawa da https://

™ HTTP: ba shi da tsaro
™ HTTPS: kuwa yana da tsaro (🔒)

™ HTTP: Bayanai suna tafiya a bayyane
™ HTTPS: kuwa bayanai a ɓoye suke tafiya (🔒)

™ HTTP: Cikin sauƙi Hacker zai iya ganin bayanai
™ HTTPS: kuwa da wahala Hacker ya samu wasu bayanai (🔒)

📌 Shawara:
Kada ka saka Passwords ko ATM details a website wanda ya fara da http://. Ka tabbatar website yana da 🔒https://: kafin ka yi gangancin saka muhimman bayananka.

Ku yi following ɗin Abba Umar Khetry domin samun muhimman shawarwari da haske akan Tech & Cyber Security.


Abba Umar Khetry ™

Sau Tari Mutane Masu Kwaɗayi, Da Mutane Masu Saɓon Allah, Sun Fi Samun Matsala A Internet!Kamar yadda ake tarkon kifi a ...
13/05/2026

Sau Tari Mutane Masu Kwaɗayi, Da Mutane Masu Saɓon Allah, Sun Fi Samun Matsala A Internet!

Kamar yadda ake tarkon kifi a ruwa, haka Hackers ke ɗana tarkonsu akan mutane. Ana saka kwandon kamun kifi a ruwa, a makale abinci domin jan hankalin kifaye su faɗa a k**a su. Haka Hackers ma suke amfani da abubuwa masu jan hankali domin yaudarar mutane.

Sau da yawa mutane masu kwaɗayi, da mutane masu saɓon Allah, misali: masu bibiyar shafukan batsa, Hackers sun fi samun nasara akansu.

Galibi Hackers suna amfani da:

•™ Links na bogi (ƙarya, kyautuka, batsa d.s)

•™ Saƙonnin “Ka ci kyauta!”

•™ Fake login pages

•™ Apps marasa aminci (misali: Free VPNs ko Apps na samun kyautar data ko airtime)

•™ Saƙonnin gaggawa e.g “Account ɗinka zai kulle ka turo OTP ko ka tura wasu bayanan sirri a gyara maka, d.s”

Da zaran mutum ya danna fake link, ko kuma ya shigar da password ko bayanansa na sirri, kai tsaye zai iya shiga hannun masu Kutse.

Don haka, kafin ka danna kowanne link:

•™ Ka binciki URL ɗin sosai (HTTP = maras tsaro, HTTPS = mai tsaro)

•™ Kada ka saka password a shafin da ba ka yarda da shi ba

•™ Ka guji downloading apps daga wuraren da ba official ba

Ka yi tunani kafin ka shiga kowane shafi a Internet, domin kuwa ba dukkan abin da ke kyalli bane zinariya ba.

Allah Tsare Mu.

Abba Umar Khetry

11/05/2026

Duk mai son zama Ethical Hacker, ya koyi Programming, Networking da kuma Termux. Hacking ba wasa bane, aiki ne tukuru da juriya.

09/05/2026

Ko ka taɓa amfani da wannan Codes ɗin **21*0000 # da kuma #21 #? Ka duba comments section don ƙarin bayani💥

Ko Wani Ya Taɓa Sauraron Kiranka a Bayan Idonka?Call Forwardings yana nufin a tura kira daga wata lamba zuwa wata. Ma'an...
07/05/2026

Ko Wani Ya Taɓa Sauraron Kiranka a Bayan Idonka?

Call Forwardings yana nufin a tura kira daga wata lamba zuwa wata. Ma'ana, idan misali kana da layi guda 2, kana iya tura duk kiraye-kirayen layin farko zuwa na biyu, fa'idar – don kar a rasa kira masu mahimmanci, ko don rashin caji ko ba network a ɗayan wayar, ko kuma don tafiyar da harkokin kasuwanci da sauransu.

Babban matsalar: da an samu kuskure wani ya saci inuwar mutum zai iya Forwardings na duk kiransa zuwa layinsa, duk wanda ya kira sa, kai tsaye kiran zai iya shiga wayarsa.

Don haka, Call Forwardings yana da matuƙar mahimmanci idan an yi amfani da shi a gun da ya dace, haka kuma haɗari ne da karya doka idan an yi ba bisa ka'ida ba.

✓ Ka danna * #21 # don ganin idan akwai masu bibiyarka.

✓ Ka danna # #002 # don cire duk wata lamba da ta yi linking da layinka.

✓ Don saita tsarin ka shiga Settings, haka kuma za ka iya yin amfani da *21*lambarka #.

Idan kuwa ka yi Forwardings zuwa invalid lamba, misali “0000” ko mak**ancin haka to duk wanda ya kira ba zai same ka ba!

Domin samun ire-iren waɗannan muhimman abubuwa ku kasance tare da ni a wannan shafin.

Allah ba mu alkhairi; mu kwana lafiya.

Abba Umar Khetry

AlhamdulillahRuwan Sama na Farko a Shekarar 2026💥Litinin, 04.05.2026 @ Khetry - May...
04/05/2026

Alhamdulillah
Ruwan Sama na Farko a Shekarar 2026💥
Litinin, 04.05.2026 @ Khetry - May...

Ko ka Taɓa Amfani da VPNs?VPN (Virtual Private Network) wata fasaha ce da ke ɓoye bayananka (data) yayin da kake amfani ...
02/05/2026

Ko ka Taɓa Amfani da VPNs?

VPN (Virtual Private Network) wata fasaha ce da ke ɓoye bayananka (data) yayin da kake amfani da internet.

VPNs na: ɓoye Location da kuma IP address ɗinka, kare bayananka daga hackers, sannan yana tsare sirrinka da duk abinda kake yi a Internet.

VPN yana haɗa ka da server na daban (na ƙasa ko waje), duk abin da kake yi a Internet zai bi ta wannan server, don haka, za a dinga ganin k**ar kana wata ƙasa ta daban.

Bisa doka ana iya amfani da VPNs a:

✓ Lokacin amfani da Public Wi-Fi, misali: Internet na Cafés, Schools, Airports da sauransu, hakan zai kare mutum daga sharrin hackers.

✓ Lokacin da kake buƙatar sirri: Idan ba ka son a ga abin da kake yi a online da location ɗinka a Internet, ka yi amfani da VPN.

✓ Lokacin shiga wasu websites: Sites na wasu ƙasashe sometimes a kulle suke; ta yadda mazauna ƙasar kaɗai ke da ikon shiga, za ka iya amfani da VPN ka kulle location ɗinka ya koma na ƙasar, hakan zai ba ka damar shiga website ɗin.

Ka sani ba duka VPNs suke da tsaro ba, mostly Free VPNs na iya tattara bayananka, su kwace ko su sayar. Saboda haka, ka zaɓi VPN mai tsaro, kuma mai aminci.

Haka kuma, ka tabbatar kana amfani da shi a wurin da ya dace. Don wasu hackers na amfani da shi wajen ɓoye location, sirri da kuma kutse, wanda hakan ya saɓa doka.

Allah Kare Mu.

Abba Umar Khetry

• Don duba bayanan wayarka?• Don ganin recent apps da duk inda aka shiga a wayarka, ko da an goge su ko an sake kunna wa...
01/05/2026

• Don duba bayanan wayarka?

• Don ganin recent apps da duk inda aka shiga a wayarka, ko da an goge su ko an sake kunna wayar?

• Don canja ƙarfin network na ka, misali daga 3G zuwa 4G?

Kai tsaye, ka shiga Testing Menu ta hanyar DialPad, sai ka danna:

* #* #4636 #* #*

Wannan zai baka damar ganin wasu bayanai na fasaha k**ar network, battery, da usage statistics.

A kula: Kada ka canza settings idan ba ka fahimci abun ba, domin hakan na iya shafar yadda wayarka ke aiki.

Allah Taimaka.

Abba Umar Khetry

Address

Karkarku, Sandamu
Daura

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abba Umar Khetry posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share