Abba Khetry

Abba Khetry Tech • Security • Internet

05/06/2026

Idan kana son downloading na vedio daga kan Facebook.

30/05/2026

Yadda ake adana lambobi a cikin Email.

28/05/2026

Idan kana a yanayin
da ba ka son ɗaga kira,
kuma kana son aiki
da wayarka.......

Barka da Sallah ♥️😅⁦♥️⁩تقبل الله منا و منكم؛ عيد مبارك
27/05/2026

Barka da Sallah ♥️😅
⁦♥️⁩تقبل الله منا و منكم؛ عيد مبارك

24/05/2026

Yadda za ka dawo da abubuwan da ka goge a wayarka.

22/05/2026

Idan budurwarka ta saka ka a BLACKLIST, ko saurayin ki yayi BLOCKING na ki.

19/05/2026

Ina Masu MTN da AIRTEL 💥

Shin Websites Kamar Facebook Suna Ganin Passwords Ɗin Mutane?Mafi yawan Websites masu tsaro suna amfani da HASHING: wata...
19/05/2026

Shin Websites Kamar Facebook Suna Ganin Passwords Ɗin Mutane?

Mafi yawan Websites masu tsaro suna amfani da HASHING: wata fasaha ce da ke canza Password zuwa wani Code na Sirri, yadda ko ma’aikatan Website ba sa ganin ainihin Password ɗinka kai tsaye. Haka kuma, a mafi yawan lokuta ba a iya mayar da Hashed Password zuwa Readable Password cikin sauƙi.

Sai dai, wasu Websites marasa kyau na iya ajiye Password ɗinka yadda ka rubuta shi kai tsaye a database ɗinsu. Idan aka yi Hacking ko aka samu matsalar tsaro, za a iya ganin Passwords ɗin mutane tsirara yadda aka rubuta su.

❗Ka kula: Ba duk Website mai http:// ne maras tsaro ba, haka kuma https:// 🔒 ba yana nufin Website ɗin amintacce ne ɗari bisa ɗari ba. HTTPS kaɗai yana kare bayanai yayin tafiya tsakanin kai da Website, amma har yanzu Website ɗin na iya zama na Bogi ko Phishing.

SHAWARA...
™ Ka daina amfani da Password iri ɗaya a mabanbantan shafuka.

™ Ka dinga amfani da Passwords masu ƙarfi.

™ Ka kunna 2-Factor Authentication a kowanne Account.

Kuyi following ɗin Abba Umar Khetry domin samun shawarwari da kuma haske akan Tech & Cyber Security 💻🔐

📞 Shin Ka Taɓa Lura Wasu Lokuta Haka Siddan Ana Cire Maka Kuɗi Babu Gaira Ba Saba?Haka kawai sai ka ji mutane suna ƙoraf...
16/05/2026

📞 Shin Ka Taɓa Lura Wasu Lokuta Haka Siddan Ana Cire Maka Kuɗi Babu Gaira Ba Saba?

Haka kawai sai ka ji mutane suna ƙorafi akan katinsu ba ya daɗewa, ko ana sace musu wani kaso da zaran sun loda, kana mamakin dalilin da yasa ake cire musu kuɗi a layi ba tare da sun yi kira ko sun sayi data ba 😳

DALILIN SHI NE:
Lokuta da dama mutane suna Subscriptions na wasu Services da ake tallata musu ba tare da sun sani ba.

Wannan Code ɗin *305 # zai taimaka maka wajen:

✅ Duba Services da aka kunna a layinka,

✅ Ganin Services masu cire maka kuɗi,

✅ Dakatar da su duka, ko cire duk wanda ba ka buƙata.

📌 Ka tuna: *305 # yana aiki a dikkan kamfanonin layika da ag-garemu a Nigeria.

⚠️ SHAWARA: Duk lokacin da ka yi arba da sabon Saƙo ka tsaya da kyau ka karanta, domin sau tari tallace-tallace ne, kuma wasu tsarukan su ke sa ana cire mana kuɗi a waya.


Ku yi following ɗin Abba Umar Khetry domin samun shawarwari da kuma haske akan Tech & Cyber Security.

Abba Umar Khetry ™

Shin Ka Taɓa Tunanin Wani Zai Iya Ganinka, Da Sauraron Duk Abinda Kake Tattaunawa A Wayarka 😂?Eh, tabbas akwai yiwuwar h...
15/05/2026

Shin Ka Taɓa Tunanin Wani Zai Iya Ganinka, Da Sauraron Duk Abinda Kake Tattaunawa A Wayarka 😂?

Eh, tabbas akwai yiwuwar hakan a wasu lokuta.

Meyasa kake shiga da waya banɗaki?
~ Saboda akwai Network 😂

Meyasa ka saki jiki har kuke tattaunawar sirri a waya ko kuma wayar na kusa da ku?
~ Saboda ka cire Handsfree 😂

Ke! Meyasa kika tura wa miji ko saurayinki saƙo ta Messenger?
~ Saboda ba Ɓaci😂

Ƙaddara ma ba ɓaci, ka sani wasu apps marasa aminci ko malware na iya neman izinin amfani da Camera ko Microphone a waya. Idan an ba su Permission ba tare da la'akari ba, akwai yiwuwar su yi amfani da su fiye da yadda ake zato.

Idan wani ya samu damar sarrafa wayarka, hakan na iya ba shi damar gani da sauraron duk wani sirri na ka!

Don haka, ya kamata kowa ya kula da abubuwan nan:

™ Ba kowane App ake ba Permission na yin amfani da Camera ko Microphone ba.

™ Ka kula da yadda wayarka ke yin zafi ko saurin ƙarewar caji ba tare da amfani mai yawa ba.

™ Kuma ka kula da Indicator na Camera ko Microphone a saman Notifications na wayarka.

✓ Yadda Zaka Kare Kanka™:

✅ Ka riƙa duba Permissions na Apps akai-akai (duk wani App dake da Permission na yin amfani da Camera ko Microphone ka tabbatar yana da aminci).

✅ Kada ka sauke Apps daga wuraren da ba ka yarda da su ba.

✅ Ka riƙa Updating na wayarka da Apps lokaci bayan lokaci. Sannan ka goge duk Apps ɗin da ba ka amfani da su ko waɗanda ba ka yarda da su ba.

NOTE: Ba duk lokacin da waya ta yi zafi ko batiri ya ragu bane Hacking. Amma yana da kyau a kula da duk wani sauyin da ba a saba da shi ba.

Ku yi following ɗin Abba Umar Khetry ™ domin samun muhimman shawarwari da haske akan Tech & Cyber Security.

Abba Umar Khetry ™

Address

Karkarku, Sandamu
Daura

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abba Khetry posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share