Abubakar Isah

Abubakar Isah Personal Blog | News Updates | Business Advertisements
Follow for daily updates and opportunities.

Bayan shiga kwankwasiyya da gawuna yayi  Yanata Kwaso masoyansa cikin tafiyar.Jagora kwankwaso ya wanke gawuna Daka dukk...
15/05/2026

Bayan shiga kwankwasiyya da gawuna yayi Yanata Kwaso masoyansa cikin tafiyar.

Jagora kwankwaso ya wanke gawuna Daka dukkan Zargi da ke masa Jagora yakara maimaitawa cewar : Gawuna be taba cimasa mutunci ba.

Kuma sannan ba tin Yanzu ba gawuna yake kokarin dawowa gurin jagora,Tin Lokacin d Ganduje ya butulce Amman jagora yace ya zauna Suci dadi. Adalci irin na jagora kenan.

tsohuwar magana ce. Jagora ne yace masa ya dakata tukunna se Yanzu lokaci yayi.

Jagora Yace : Insha Allahu Gawuna da kwankwasiyya mutu ka raba. Daman jagora yafada Tin a baya Gawuna be taba Chanza yadda yake girmama shi ba duk da ba’a Inuwar Jam’iyya guda daya.

Jagora yayi wannan maganar Ne Lokacin da Gawuna yake ta kawo magoya bayansa Domin yin Mubayi’a Ga jagoran Darikar kwankwasiyya.

Abdallah karwai✍🏽
15/5/2026

"Dama ai falle ɗaya ce a jam'iyyar NNPP, kuma za mu yi falle na biyu a APC, ita kuma jam'iyyar ADC da su ka koma, ko fal...
06/04/2026

"Dama ai falle ɗaya ce a jam'iyyar NNPP, kuma za mu yi falle na biyu a APC, ita kuma jam'iyyar ADC da su ka koma, ko falle ɗaya ba za ta yi ba har abada" - Gwamna Abba.

YANZU-YANZU: Allah ne ke bayar da mulki, amma Kwankwaso shi ne ɗan siyasar da ke da tasiri wajen yanke hukuncin wanda ke...
05/04/2026

YANZU-YANZU: Allah ne ke bayar da mulki, amma Kwankwaso shi ne ɗan siyasar da ke da tasiri wajen yanke hukuncin wanda ke lashe zaɓen shugaban ƙasa a Nijeriya. Saboda Kwankwaso ne na sha kaye a zaɓen 2015, in ji Goodluck Jonathan.

Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu na iya fāɗuwa a zaɓe idan Rabiu Musa Kwankwaso ya koma gefen Atiku Abubakar. Ya ce yawan gwamnoni ba lallai ba ne ya hana ɗan takara shan kaye a lokacin zaɓe.

Goodluck Jonathan ya ce:
“A zaɓen shekarar 2015, ina da gwamnoni 28 a bayana, tare da mataimakin shugaban ƙasa daga Arewa maso Yamma. Duk da wannan fa’ida ta siyasa, sak**akon zaɓen ya nuna akasin haka, domin Kwankwaso ba ya tare da ni, kuma hakan ya sa na sha kaye a hannun Muhammadu Buhari.”

Ya ƙara da cewa:
“A yau ma, ina ganin wani yanayi mai k**a da wannan. Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da gwamnoni 30 da ke mara masa baya, tare da mataimakin shugaban ƙasa daga Arewa maso Gabas. Sai dai ina ganin idan Kwankwaso bai shiga jam’iyyar APC ba, hakan na iya shafar nasarar Tinubu a zaɓen 2027.”

Ku yi following Jaridar ATV Hausa.

An k**a wani matashi da ya sanya kayan soja na bogi a Angwan Rukuba, Jihar Plateau,sunansa Ezekiel Joseph ne, ba Yohana ...
05/04/2026

An k**a wani matashi da ya sanya kayan soja na bogi a Angwan Rukuba, Jihar Plateau,
sunansa Ezekiel Joseph ne, ba Yohana Audu ba k**ar yadda wasu rahotanni ke yadawa.

Jami’an ‘yan sanda ne s**a cafke shi yayin da yake sanye da kayan sojoji, kuma aka same shi dauke da katin shaidar makarantar sojin Najeriya (Nigerian Military School) na bogi.

Wannan kamen yana da alaka da harin ranar Palm Sunday da aka kai a unguwar Angwan Rukuba, inda sama da mutane 30 s**a rasa rayukansu.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Plateau ta tabbatar da k**a Ezekiel Joseph tare da wasu mutane shida da ake zargi da hannu a harin. A halin yanzu, jami’an tsaro na gudanar da cikakken bincike domin gano dukkanin wadanda ke da hannu a wannan hari da kuma rushe cibiyar da ke bayansa.

Da Addini Ake Shirya Jana’izarmu!Akwai wani mataki da in jahilcinka ya kai to hakan yana zama babban makami ne a hannun ...
05/04/2026

Da Addini Ake Shirya Jana’izarmu!

Akwai wani mataki da in jahilcinka ya kai to hakan yana zama babban makami ne a hannun makiyanka.

Abin da yake faruwa a Najeriya a halin yanzu, musamman abubuwan da s**a shafi rikicin Jos da sauran sassan kasar nan, ba yaki ne na neman gaskiya ko bayyana ta ba; Surgical Operation ne da aka kera don raba zuciyar talaka musulmi da talaka kirista.

Kafin bayyanar wadannan mutane biyu da kuke gani, musamman wannan bako mai suna Alex, al’ummar kasar nan suna da wani tsari na Tolerance (hakuri da juna). Sun san cewa duk wanda zai biyo dare ya kashe mutane, bazai tambayeka addini ba kafin ya harba harsashi.

Amma yau, an shigo da gubar da take nuna wa kowane bangare cewa shi kadai ake nema a kashe, musamman kiristoci sunfi Shan wannan gubar duk da sanin gubar zatayi musu illa anan gaba.

Wannan bawan Allah mai suna Alex yana tafiya ne da ajandar da muke kira Divide and Rule (Raba ka mulka). Yana rura wutar cewa wai kiristoci ne kawai ake hara, alhalin gaskiyar magana ita ce, harsashin bindiga baya zabar fata ko aqida; musulmi ma kashe su ake yi, kiristoci ma ana kashe su.

Abin bakin ciki shi ne, idan wannan wutar ta Religious War tafi karfin kiristocin, Alex fa ba zai tsaya ya gani ba, Kuma bazai tsaya ya karesu ba. Yana da Dual Citizenship, yana da International Passport. Da zarar jini ya fara malala a titunan Jos ko Kaduna, zai dauki kayansa ya koma kasashen waje ya bar ni da kai muna karar da kanmu, k**ar yadda na samu Labarin harya gudu ya barmu.

Yakin addini ba k**ar harin ‘yan ta’adda ba ne; ‘yan ta’adda suna bugawa ne su gudu, amma yakin addini ciwo ne da yake zama a gida, yana tashi da safe, ya kwanta daddare, kuma babu gwamnatin da ta isa ta tsayar da shi muddin zuciya ta riga ta baci.

Ya k**ata mu tambayi kanmu: Wane ne yake cin ribar wannan?

Ilimin Physics ya koya mana cewa duk inda aka samu Friction (gogayya), to ana samun Heat (zafi). Wannan zafin da suke samarwa a tsakaninmu shi ne yake ba su damar cigaba da satar😡

Address

Bauchi
Azare
751101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abubakar Isah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share