01/08/2026
🛡️ Su Waye White Hat H$ckers?
White Hat H$ckers mutane ne da suke amfani da iliminsu na Cybersecurity da Ethical H$cking domin kare kwamfuta, Networks, da Websites, ba don cutarwa ba sai don su taimaka.
Ayyukansu sun haɗa da:
1. Gano raunin tsaro (Security Vulnerabilities) kafin blackhat h$ckers su gano.
2. Yin Pe*******on Testing domin tabbatar da tsaro.
3. Taimakawa kamfanoni da ƙungiyoyi wajen ƙarfafa tsaronsu.
4. Bayar da rahoton duk wata matsalar tsaro da s**a gano (Reports).
5. Taimakawa wajen hana hare-haren yanar gizo (Cyber Attacks) da satar bayanai.
🟢 White Hat H$ckers ba sa yin h$cking ba tare da izini ba. Kafin su gwada tsaron kamfanoni, sai an basu izini tukunna, kuma suna bin doka da ƙa'idodin Ethical H$cking.
Yanzu manyan kamfanoni, bankuna, gwamnati, etc suna amfani da White Hat H$ckers domin gano matsalolin tsaro kafin Blackhat su gano suyi amfani da su wajen h$cking dinsu.